Labarai

Spread the love

SHUGABAN TURKIYYA YA KALUBALANCI MATAKIN SAUDIYYA AKAN QATAR

-Wannan Ba koyarwar Musulunci BaneĀ 

Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan yayi Allah Wadai da Mayar da kasar Qatar saniyar-ware da Makwabtanta keyi, inda yace hakan ya keta koyarwar Addinin Islama. Kazalika yace wannan mataki daidai yake da yankewa ita Qatar din hukuncin Kisa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan jawabi na shugaban na Turkiyya ya kasance shine sanya baki na farko da wata kasa dake da karfin fada aji tayi a cikin kwanaki takwas da yiwa Qatar Dangwal-Fulako wadda kasar Saudi Arabiya take jagoranta.

Kasar Qatar dai ta musanta irin kalamai da kasashen Saudiyya da yan kanzaginta suke tuhumarta dasu, na daure gindi ga yan ta’adda da kuma kasar Iran.

Matakin takunkumi da aka kakabawa kasar ta Qatar mai arzikin man fetur dake da Yawan mutane Miliyan 2.7, ya kawo tsaiko akan shigar da kayan abinci da sauran kayan masarufi cikin kasar, duk da cewa ana cikin watan Azumi.

Yanzu haka dai, kasar wadda ke shigar da kashi 80 na abincinta daga manyan kasashen yankin Gulf kafin wannan mataki, ta koma yin magana da kasashen Iran da Turkiyya domin neman abinci da ruwa.

“Wannan mataki ne da aka dauka mai tsauri akan Qatar, inda aka maida wannan kasa saniyar ware kuma hakan ya sabawa koyarwar addini. Wannan tamkar hukuncin kisa ne aka yankewa Qatar,” Erdogan yayi wannan bayanine ga yan Jamiyya mai mulki ta AK a birnin Ankara.