Mulki Da Fatalwa: Yawan Matattu Da Aka Bawa Mukami A Gwamnatin Buhari Sun Karu

Spread the love

Yawan mutanen da Shugaba Buhari ya nada domin rike mukamai a gwamnatinsa da aka tabbatar sun mutu yanzu haka ya karu zuwa 7 daga 3 da aka bayyana da farko.

Tunda farko dai an gano Marigayi Donald Ogbaja, wanda aka nada a matsayin mamba a Majalisar kare hakkin masu ciniki, sai kuma Chris Utov da aka kai Hukumar Bincike akan Tattalin Arziki da zamantakewa, inda na ukun shine Sanata Okposu wanda yake shugabantar Majalisar Kula Da Yanjarida.

Bayan da aka kara nutsa na mujiya akan wadancan sunaye da Gwamnatin Tarayya ta fitar sai aka kara gano sunayen wasu matattun wadanda suka kunshi Marigayi Garba Attahiru Da Marigayi Umar Dange, Sai kuma wata mace Marigayiya Madgalene Kumu wadda tuni aka nada a hukumar tace fina-finai.

Kakakin Fadar Shugaban |kasa Mallam Garba Shehu dai ya fito ya bayyana lamarin a matsayin kuskure irin na biladam, inda ya kuma kara da cewa wannan lissafi na mutane anyisu ne tun shekarun baya lokacin Babachir Lawal yana kan kujerar Sakataren Gwamnati. Yace Irin dan jinkiri da aka samu wajen yin nadin shine ya kawo akayi kitso da kwarkwata.