Yadda Kankana Ke Yakar Jinyoyi Da Suka Addabar Al’umma

Spread the love

Daga Yunusa Kumo

Kankana na daya daga cikin irin wadannan nau’o’in abinci da Allah ya yassarewa dan Adam don kara lafiya da kare garkuwar jikinsa.

Binciken masana daban-daban akan wannan dan ice na kankana ya bayyana cewa ba kasafai ake samun dan ice mai matukar fa’ida da alfanu ga dan Adam ba irin kankana.

Binciken nasu ya gano cewa kashi casa’in cikin dari (90%) na kankana duk ruwa ne. Amma sai dai Allah ya albarkaceta da dimbin sinadarai masu matukar fa’ida ga jikin bil’adama. Tana dauke da sinadaran kariyar jiki irin su vitamin A da vitamin B6 da kuma vitamin C. Sannan tana dauke da sinadaran lycopene da antioxidants da kuma amino acid wadanda suka kai matuka wajen gyaran jiki.

Binciken ya bayyana cewa kankana tana taimakawa wajen magance matsalolin ciwon zuciya da hawan jini da kansa da kuma kaba.

Masanan sun bayyana cewa kankana tana taimakawa masu shanta wajen kara karfin ido da gyara fata tayi sumul-sumul tana sheki, gashi kuma takan taimaka wajen gyaran gashi tasa yayi laushi.

Masanan sun bayyana cewa shan kankana musamman ga tsofaffi yakan taimaka wajen magance matsalolin cushewar jijiyoyin jini da yamutsewar fata.

Ga masu aikin karfi ko motsa jiki kuwa, binciken masanan ya gano cewa shan dan icen na kankana na taimakawa wajen rage tsamin jiki wato gajiya.

Shima dai wanda yar gusau ta koroshi, masanan sun gano cewa shan kankanan na iya taimakawa cikin gaggawa wajen kauda ita.

Wassu fa’idojin kuma da masanan suka bayyana na kankana sun hada da cewa tana taimakawa wajen wanke koda, narkar da abinci a kan lokaci, rage zafin jiki, taimakawa wajen warkewar rauni da wuri, kara karfin dasashi da kuma garkuwar jiki.

Sai dai masanan sunyi gargadin cewa shan kankanar ya wuce kima kan iya janyowa mutum kumburin ciki, murda harma da amai.

Sannan sun shawarci mashayanta da masu shirin farawa da cewa su darje su zabi wacce ta nuna tayi jajir, domin kuwa irintace ke dauke da dukkannin sinadarai masu muhimmancin da jiki ke bukata.

To ko don me kake shan kankana?

Sagir Shitu wani mai shan kankana ne, kuma yace yana shanta ne don takan taimaka wajen magance cutar basir musamman game maza. Ta bangaren mata kuwa takan taimaka musu matuka wajen gyaran jiki.

Anfanin kankana dai ba ga lafiya kadai ya tsaya ba, domin harma takan taimaka wajen rufin asiri da dogaro da kai. Dinbin matasa da magidanta ne dai ke dogara da ita wajen biyan bukatun yau da kullum.

Ta fuskar tattalin arziki ma ba’a bar kankanar a baya ba, don kuwa ana safararta musamman daga arewacin kasar nan zuwa kudanci. Sannan har sarrafata akeyi izuwa ta gongoni, al’amarin da yake taimakawa matuka wajen samawa matasa aiki.

Ita dai kankana nagge ce dadi goma, domin kuwa ba abin jefarwa a jikinta; kama daga tsokanta, ‘ya’yanta harma da bawonta, don kuwa suna dauke da dimbin sirruka da wassu ma ba’a gano su ba kawo yau.

Kankana dai tana da nau’o’i sama da dari uku, amma daga ciki nau’o’i hamsin ne kawai suka fi shahara.

‘Yan azancin magana dai na cewa “kaci abincinka a matsayin magani, inko ba hakaba zakaci magani a matsayin abincinka.”