Yadda Sarkin Swazi Ya Auri Mace Ta Goma Sha Hudu (14)

Spread the love

Amaryar  Sarkin Swazi Mswati III

Sarkin kasar Swazi dake Afirka ta kudu Mswati III ya auri yarinya yar shekaru 19, Siphelele Mashwama, Wadda ‘ya ce a wajen Ministan kasar, Jabulile MashaAllah a matsayin mace Ta 14.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa hakan ya biyo bayan satittika na cece-kuce da yamididi.

Mai kula da bukukuwan sarauta na masarautar, Hlangabeza, Yace yanzu haka Amaryar tana birnin New York na Amurka, inda Sarkin mai shekaru 49 ya halarci taron majalisar Dinkin Duniya.

Matan Sarkin su hada, Inkhosikati LaMatsebula, Inkhosikati LaMotsa, Inkhosikati LaMbikiza, Inkhosikati LaNgangaza, Inkosikati LaMagwaza (deserted), Inkhosikati LaHoala, Inkhosikati LaMasango, Inkhosikati LaGija.

Sauran sune,  Inkhosikati Magongo, Inkhosikati LaMahlangu, Inkhosikati LaNtentesa, Inkhosikati LaNkambule, Inkhosikati Ladube and Inkhosikati LaFogiyane.

Sarki  Mswati, wanda akewa lakabi Ngwenyama, “zaki,” ance yana da yaya 13, wadanda suka hada da yar sa ta fari  Gimbiya Sikhanyiso, Sibahle Dlamini, Makhosothando Dlamini, Majaha Dlamini, da Tiyandza Dlamini.

Sauran sune, Sakhizwe Dlamini, Saziwangaye Dlamini, Bandzile Dlamini, Lindaninkosi Dlamini, Mcwasho Dlamini, Temtsimba Dlamini da Temaswati Dlamini.

Ba bakuwar al’ada bace Sarkin kasar Swazi Ya zabi mace duk shekara. Shekarar da ta gabata Sarkin ya zabi mace ne yayin rawar al’ada ta shekara – shekara da ake kira Umhlanga.

Yan matan Swazi yayin Rawar Umhlanga 

 

A kasar Swazi dubban mata ne da basu da aure da marassa yaya kanyi tururuwa daga sassan kasar domin zuwa Ludzidzini, inda ake Kwashe tsawon kwanaki 8 ana chashewa, kuma za’a duba budurcin matan da za’a Yiwa Aure.

Kasar Swazi dai a yanzu itace kasa daya tilo da take kan tsarin Sarauta zalla a duniya.

Kamar yadda Unicef ta kididdige, kasar itace kan gaba a duniya wajen cutar HIV. A kwai sama da mutane 210,000 dake dauke da cutar kanjamau