Buhari Ba Zai Samu Takara Ba A 2019 – Ango

Spread the love

Farfesa Ango Abdullahi yace Buhari Ba Zai Samu Takara Ba kai tsaye domin tsayawa jamiyyar APC a Zaben shekara ta 2019. Shugaban na zauren Dattijan Arewa yayi wadannan kalamai ne a wata hira da yayi da jaridar The Sun, inda yace kasancewar Buhari A matsayin wanda ke kan mulki yanzu ba dama bace ta ya samu takara kai tsaye, in dai har akwai tsarin siyasa ta cikin gida.

“Kasancewar ka akan kujerar shugabancin kasa baya nufin yan Jam’iyyar bazasu nemi kujera daya da kai ba. Inda ni Buhari ne, zanyi maraba da na goga da wasu a Jam’iyyar. “Wannan wata dama ce ga dimokradiya a jamiyya ta, kuma zanyi kira ga jama’a su zo su gwada farin Jinin su.

A kwanakin baya Aisha Jummai Alhassan, Ministar Harkokin Mata, Wadda ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin gwaninta, ta sha tsangwama a wurin jama’a. Amma daga bisani ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Shugaba Buhari shine ya fadawa yan Jam’iyyar sa cewa ba zai tsaya takara ba a 2019.

Goyon bayan da Ministar ta bayyana ga tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ci gaba da Jawo kace-nace a tsakanin yan Najeriya.

“A Zaben 2014/2015, Yace zai tsaya ne sau daya domin ya share dattin da yan PDP suka tara. Kuma ni na yarda da maganar sa, ba zai tsaya takara ba a 2019 “,  Inji Minista Jimmai Alhassan.