Gero Yafi Shinkafa Sinadarai Na Kare Jiki Daga Cututtuka

Spread the love

Ana amfani da Gero a matsayin sinadari na yin miya, a wasu sassan wajen yin burodi. A kasar Indiya wani Burodi mai fadi da ake kira Roti, ana yinsa ne daga fulawar Gero. A Gabashin nahiyar Turai ana amfani da shi wajen Dafa-duka da kuma kayan sha. Yayin da a Afirka akan yi amfani da shi wajen koko da burabisko.  

Mutanen duniya da dama basu da labarin Gero, bare ma su iya gane alfanunsa a kayan gina jiki. Amma duk da haka, Gero ya kasance wani sirri na Iyaye da kakanni.

An gano asalin wannan kayan Abinci ne daga kasar Sin Wato China, wanda aka shafe shekaru da dama ana amfani dashi a kasashe da dama.

Cikin wadannan dimbin shekaru, Gero ya kasance mai darajar Gaske a kasashen China, Indiya, Girka, Masar da Yammacin Afirka, inda ake amfani dashi wajen yin burodi da Couscous da kuma kamu na sha a matsayin koko ko kunu.

Amfanin Gero Na Gina Jiki 

Gero ya kunshi wasu muhimman sinadarai na gina jiki da ba’a samun su a cikin wasu nauin Abinci da muke amfani da su.

  • Magnesium a cikin Gero Yana taimakawa wajen rage kaifin Ciwon kai na Migraine da kuma bugun zuciya.
  • Niacin (vitamin B3) a cikin Gero yana taimakawa wajen rage kitse dake jikin mutum.
  • Phosphorus a cikin Gero ya taimakawa wajen narkar da kitse da kitse da muke ci, da gyara fata.
  • Gero yana taimakawa wajen saukaka hadarin cutar diabetes
  • Kazalika wani Bangaren jikin Gero yana taimakawa wajen rage hadarin sankarar nono.
  • Sannan Gero yana kare yara daga cutar Asthma.