Musulunci A Tsakanin Mubarak Bala Da Abubakar Shekau (I)

Spread the love

Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Matsalar mulhidai irin su Mubarak Bala shine sun fahimci addini irin yadda su Abubakar Shekau  suka fahimta. Addini a matsayin kisa, zubar da jini, tashin hankali, ci-baya, yakar ilimi da rashin ‘yanci. Yayin da su Abubakar Shekau ko Abubakar Albaghdadiy suke yanka mutane, su kuma suna ganin addinin shine yanka mutanen! Wannan rashin adalci ne da kuma yi wa mabiya addinai kudin goro wajen cewa suna aikata ta’addanci a matsayin addini.

Idan ko haka ne za mu iya cewa abin da mulhidai suka yi irin su Benito Mussolini na kisan kare dangi da kashe mutane a yakokinsu to shine ilhadi! Za mu iya cewa abin da muka fi tsoro a wannan zamanin, wato makamin kare dangi na Nukiliya….   1.1j4.64.mobile-gws-img  wanda Albert Einstein shi ne yayi sababin kawo shi a kimiyyance, shi ma kimiyyane!

Kuskure ne mu ce abin da Lord Resistance Army ko Adolf Hitler suka yi a Uganda koyarwar kiristanci ne. Kuskure ne mu ce zaluncin da Zionists suke yi a Isra’ila akan raunanan Palasdinawa shi ma koyarwar addinin yahudanci ne. Kuskure ne mu ce abinda wasu tsirarun ‘yan addinin Buddha suke aikatawa ga Musulman Rohingya yana nufin shine addinin.

Dukkanin wadannan addinai da na lissafa a sama suna koyar da zaman lafiya da soyayya. Sai dai a ko’ina ba a rasa azzalumai da suke fakewa da sunan wani addini ko kungiya ko ilimi wajen zaluntar raunana. Addinin Buddha na Gotama Buddha a misali an san shi da zaman lafiya da rashin neman rigima kuma akan haka ya dora falsafarsa kuma mafi yawan mabiyansa a haka aka sansu. Litattafan addinin kamar irin su “Sutta-Pitaka” da “Tripitaka” da za a iya samun bayanan Gotama Buddha a ciki, wanda an tattara su a cikin wasu mujalladan litattafai da ake kira “Sacred Books of the Buddhists”, sun nuna addinin na zaman lafiya ne da hakuri. Don haka ake mamakin ya a ka yi Adolf Hitler ya dauki tambarin addinin (swastika) da yake nuna zaman lafiya kuma ya yi amfani da shi wajen kisan kiyashin da ya ya yi wa yahudawa.

Saboda haka, samuwar irin su Ashin Wirathu ko Aun San Suu Kyi da suke taimakon kisan kiyashin da ake wa Musulmi a cikin addinin ba ya nufin cewa falsafar addinin ta koma ta tashin hankali ba ne.

Za mu zargi mutum ne da kwadayinsa na zubar da jini, amma ba addininsa da dama ya hana shi aikata hakan ba. Duk son zaman lafiyar Mohatma Mohandis Gandhi karshe dan addinin Sikh ne ya kashe shi. Shin addinin Sikh za mu zarga ko mutumin da ya yi kisan? Bayan an harba nukiliya a kasar Japan kan Hiroshima da Nagasaki, shin kimiyya da Albert Einstein za mu zarga ko kuma America da ta harba makamin?

Idan su Abubakar Shekau sun yi amfani da fasahar sadarwa (YouTube a misali) wajen tsorata mutane, shin fasahar za mu zarga ko kungiyar Boko haram?

Haka shima addinin kiristanci, kowa ya san addinin da takensa na soyayya. Yesu Almasihu dakansa ya koyar da cewa koda an mare ka to, ka juya fuskarka a kara maka don kada ka batawa mai dukan ka rai! Amma a haka ba a rasa ‘yan ta’adda a cikin addinin kamar su Adolf Hitler a Germany ko kungiyar Lord Resistance Army a Uganda ba. Shin hakan na nufin koyarwar kiristanci ne? Kiristanci daban da abinda ‘yan ta’adda suka fake da addinin suka aikata.

Dan adam yana da son rai tun asali. Duk lokacin da ya ga yana da karfi to sai ya yi kokarin cin zalin na kasa da shi. Hatta a duniyar ilhadin a haka mutane suke. Lokacin da Karl Marx ya fito yana yakar masu kudi da azzaluman addini, shi ake zalunta da raunana. Amma bayan ya samu karfi da taimakon Lenin da zuwa irin su Joseph Stalin a Rasha sai suka koma zaluntar raunana a Afghanistan da sunan kwamunisanci. Da taimakon America, kungiyar Taliban da Osama bn Laden ta yi karfi suka raunana tarayyar Soviet sai suka koma zaluntar wasu da sunan addini. A haka dan adam yake aikata abinda ya ga dama amma sai ya fake da addini ko fahimta.

Ina yi maka uzurin cewa ba ka fahimci addinin Musuluncin da aka haife ka a cikinsa ba balle falsafar sauran addinan. Ka tashi a inda ake hana tambayoyi da sunan addini kuma ake zalunci da sunan shari’a. Shari’ar da ka fahimta, irin ta Shekau, ba ita ce shari’ar Musulunci ba. Shari’ar da a ka yi a Zamfara wacce ta kyale masu satar miliyoyi daga ‘yan siyasa kuma ta yankewa barawon saniya hannu, ba ita ce shar’iar da Musulunci ya ce a yi ba.

Ubangijin da ka ke zato mai kama da mutane (anthropomorphic) ba shine Ubangijin Musulunci ba. Fahimtar da ka yi wa Allah (anthropocentric) ba ita ce fahimtar tauhidin Musulunci ba. Yakokin da ka ke cewa sahabbai sun yi, ina so ka gane cewa a tsarin dokar Musulunci aikin sahabi ba hujja ba ne. Ni a kan kaina nafi ganin abinda su ka yi a matsayin mulkin mallaka (colonialism) amma ba tsarin Musulunci da ya ce babu dole a addini ba.

Kafin ka shiga halin da ka shiga na musanta samuwar Allah da yakar addinai ni kaina na taba samun irin wannan shakkun (waye bai taba samu ba?!). Bambancina da kai shine ni ban yi gaggawar cewa shi kenan babu Allah ba. Abin da ka yi shirme ne a falsafa da ake kira “Category Mistake” wato rashin samun abu bayan ka bincika sai kace babu shi baki daya! Kuma irin wannan abin da kake shine ake kira “argumentum ad ignoratiam”, saboda ka rasa wanda zai maka bayanin abu sai ka ce karya ne! A nan ba bayani zan yi maka don ka koma Musulunci ba, bayani zan maka don ka gane baka fahimci addinin Musuluncin da ka ke yaka kuma ka ke kwatanta shi da ayyukan ‘yan ta’adda kamar Shekau ba.

Da farko zan fara nuna maka cewar addinin Musulunci ya bai wa kowa ‘yancin ya yi addininsa kuma babu dole a cikinsa ((Q2:256)). Hatta Manzon Allah (saw) ya fada a ayoyin Alqur’ani ba babu adadi cewa, da Allah yana so da ya mayar da kowa Musulmi, don haka ba ya tilasawa kowa sai ya zama mai imani da shi ((Q10:99)).

Sannan Alqur’ani ya fada mana cewa kowa yana da ‘yancin ya zabi inda ya ga damar yi amma zai tarar da hukunci a ranar lahira ((Q10:108)). Sannan a Alqur’ani ((Q4:137)) Allah ya bamu labarin wadanda suka yi imani sannan suka kafirce, sannan suka kara imani kuma suka kara kafircewa, suka kara imani sannan suka kara kafircewa! Amma ba abinda Annabi (saw) ya yi musu na kisa. Duk ba ka ga wadannan ba sai hadisi guda daya da ba ka iya rubuta shi daidai ba?! Duk ba ka ga yadda Allah ya bada ‘yancin addini a ayoyi sama da 100 ba, sai hadisi guda daya da dama ana tantamar ingancinsa? Wadanda suka aminta da ingancinsa ma sun yi tawilinsa, maimakon daukar lafazinsa (literally).

Hadisin yazo acikin “Sahihul Bukhari” da karamin littafin “Arabeen An-nawawy” da sauransu cewa Manzon Allah (saw) yace “An umarceni da na yaki ‘mutane’ har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah”. Tare da cewa hatta Ibn Hajar a littafinsa na “Fathul Bariy” a sharhin da ya yi wa “Sahihul Bukhari” ya tabbatar da cewa akwai matsala ta fuskar sanadin hadisin (sanadin hadisi shine yake nuna ingancinsa ko rashin ingancinsa ta wata fuskar). Amma koda ya inganta to, me ake nufi da kalmar ‘mutane’ a hadisin? Bisa ilimin falsafar yare (linguistic philosophy) da kuma “Logical positivism” kalmar ‘mutane’ ita ce za ta gaya mana mai hadisin yake nufi domin ayyukan Annabi (saw) ya nuna cewa dole muna bukatar sanin me kalmar ke nufi tunda Manzon Allah dai ya zauna da wadanda basu yarda Allahn shine abin bautarsu ba kuma bai yake su ba.

A cikin Madina akwai yahudawan Banu Qurayza da Banu Nadhir wadanda ba Musulmi ba ne kuma Annabi bai kashe su duka ba. Hasalima a Musulunci akwai tsarin “jizya” da wanda bai yarda da Allah ba zai dinga bayarwa don ya yi addininsa kuma a bashi tsaro da kulawa a kasar Musulunci. Da a ce gayar ko matukar abinda ake bukata shine a yi imani da Allah ko a kashe mutane dukkansu to, da babu yadda za a yi a yi sulhu da kiristocin Najran, kuma babu yadda za a yi Umar bn Khattab ya kyale coci a kasar Palasdinu!

Abinda kalmar ‘mutane’ take nufi a nan sune wadanda suka fara yakar Musulmi ba wai dukkan mutane ba. Tun asali a addinin Musulunci babu yaki sai ga wadanda suka fara yakar Musulmi ((Q22:39)) ko kuma wadanda suka kori Musulmi daga garuruwansu suka hana su ‘yancin addini ((Q22:40)). Don haka za su yaki wadannan mutane har sai ya zamana babu zalunci akan kasa kuma addini ya zama na (tsarin) Allah ((Q2:190)).

Tsarin Allah shi ne a bai wa kowa ‘yancin addininsa kuma a yi adalci, a daina zalunci a ban kasa.

Akwai cigaba.

*Wannan rubutu martani ne ga wani rubutu da wani Mulhidi Mubarak Bala ya yi a wata budaddiyar wasika da ya aikewa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, wanda aka buga a shafin NAIJ.com

Za a iya samun Aliyu Dahiru Aliyu a adireshin sa na Twitter: @aliyussufiy

Email : dahiraliyualiyu@gmail.com