Kananan Yara 15 Ake Yiwa Fyade Kullum A Kano – Yansanda

Spread the love

Yansanda a birnin Kano sun ce ana samun kararrakin fyade 10 zuwa 15 kullum a birnin. Kamar yadda wakilin Jaridar Daily Trust ya rawaito.

Babbar damuwa ga yansandan shine kasancewar duk wadanda akewa fyaden kananan yara, kuma masu laifin gaddawa ne, kamar yadda Jumimah Ayuba, shugabar Bangaren laifukan Jima’i da makamantan su, a ofishin yansanda na shahuci.

“Mun karbi kararrakin fyade masu rikitarwa a wannan ofishin. Muna da wani kara inda mahaifi Ya Yiwa ‘ya’yan cikin sa guda uku fyade. Mun kuma kama wani da yayi wa Jaririya yar wata shidda fyade”, Inji Jami’ar.

Tace irin dalilan dake kawo wannan fasadi a jihar ya kunshi mutuwar aure, tallace-tallace, rashin kulawar iyaye, mutuwa da sanya yara aikin gida.