Tsohuwar Minista A Gwamnatin PDP Sanata Oduah Tace PDP Bata Dauki Darasi Ba A Kurkuren Ta

Spread the love
 

Sanata Stella Oduah Tace har yanzu jamiyyar PDP tana maimaita Kurkuren da suka haddasa faduwar ta a zabukan shekara ta 2015.

Tsohuwar Ministar Wadda itace Sanata mai wakiltar Anambra ta Arewa ta bayyanawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa jamiyyar ta fara kakabawa mutane yan takara akan tilastawa.

Oduah, Wadda tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama ce, ta Rubuta korafi ga shugabanin Jam’iyyar, inda ta shaida musu cewa ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da Zaben fidda gwani.

Tace masu gudanarwar sun nuna wariya tsakanin yan takara da masu kada kuria.

“Har yanzu ina jiran Jam’iyyar ta dauki mataki akan korafin da na gabatar, tsarin mulkin jamiyyar ya fayyace yadda za’a gudanar da Zaben fidda yan takara”.

Ta jaddada cewa a kullum akan samu wata matsala idan aka hana yan Jam’iyyar damar su ta zabe, ta kara da cewa irin wannan hali na dauki dora shine matsalar da ta dulmuyar PDP a baya.