Tilas Malaman Sakandare A Kano Su Sayi Na’urar Dora Karatu

Spread the love


Daga Nasiru Salisu Zango
Malaman makarantun sakandare a jihar Kano na cikin halin tsaka mai wuya bisa yadda suka ce an fito da wani sabon fi’ili na tilastawa kowanne malami sayen wata na’urar tablet ko yana so ko baya so.

Wani fom da aka rararrabawa malaman ya nuna cewar wai an kirkiro wannan tsari ne domin inganta tsarin ilimin sakandare a zamanance,dan haka duk malamin da ya kai matakin albashi na 9 to lallai sai ya fanshi wannan na’ura wacce kudinta ya kai naira dubu 96.

Tambayardai ita ce, shin dama ana ciniki dole, shin farashin da aka saka yayi daidai da muradin malaman ? ko dai hanyar samun kudi wasu ke yiwa kansu ?

Malamai da dama na kukan cewar albashin su baya iya isar su,dan haka da bashi suke karasa wata, amma maimakon a fito musu da hanyoyin da zasu inganta rayuwarsu sai a ringa dora su a keken bera domin samu daga jikinsu.