Tarar Goyon Babur A Kano: Haraji ne Ko Tsaro?

Spread the love

Hukumar kula da zurga-zurgar ababen hawa ta Kano Karota ta fara cin tarar Naira 10,000 ga duk wani mai Babur da yayi goyo a bayan babur dinsa.

Ita dai wannan doka ta Haramta goyon babur an kirkiro ta ne a tsohuwar gwamnatin Kano ta Rabiu Musa Kwankwaso domin dakile kaiwa hare-hare da yan Boko Haram keyi da Babura. To amma Hukumar ta Karota ta karkade wannan doka inda take kame irin wadannan masu laifukan, ta kuma ci tarar Naira Dubu Goma.

Manajan Daraktan hukumar ta KAROTA Muhammad Hadi Zarewa ya bayyanawa manema labarai da makasudin wannan samame.

Hadi Zarewa yace sun dauki matakin ne domin inganta tsaro a fadin jihar Kano baki – daya.

Sai dai kuma a bangaren al’umma musamman wadanda abin ya sha fa suna kallon dawo da dokar a matsayin wani salo na karbar haraji daga duk wanda aka kama da laifin saba dokar, domin ana cin-tarar da ta kai kimanin naira dubu goma (#10,000) ga duk wanda aka kama da yin goyo akan babur.
Gwamnatocin Jihohi dai a Najeriya na fama da kamfar kudaden shiga, lamarin da ya haddasa gaza biyan albashi ga wasu maaikatan jihohi. Duk da cewa Jihar Kano Tayi fice a harkar kudaden shiga, abubuwan da take tarawa basu kai na Jihar Lagos ba.