Saudi Arabiya Ta Fara Dinke Baraka Tsakanin Shi’a Da Sunni

Spread the love

Ga Alamu an fara samun sauyi akan irin kiki-juna dake faruwa tsakanin kasar Saudiyya da Musulmi mabiya mazhabar Shi’a Da kuma Jagorarsu, kasar Iran. An dai shafe shekaru Gidan Sarautar Saudi Arabiya yana jagorantar shelar kin Jinin Mabiya Shi’a. Kafafen yada labarai na gidan Sarautar kan gabatar da shirye-shirye na yakar Rafidhawa da hakan ta sanya ake musu ganin tamkar ba Musulmi na kwarai ba.

Amma a wannan shekara an samu banbanci akan matsalolin aikin Hajji, inda aka bawa kowa dama, kuma ba a samu wata hatsaniya ba in bayan samu karuwa da akayi ta mahajjata da kashi 20. Kasar Iran ta kafa tarihi wajen godewa gwamnatin Saudiyya.

Tun hawan mulkin su a shekara ta 2015, Sarki Salman Bin Abdulaziz da karamin dansa kuma ministan Tsaro, Muhammad, suka sanya kafar Wando da Iran akan sai sun ga durkushewar tagomashin ta a yankin Gabar ta tsakiya da karfin tuwo. Sun kapsa da kewayen Iran Houthawa  dake Yemen, wadanda suka kwace mulkin birnin Sana’a. Sun ki amincewa bukatar biyan diyya na darururuwan mahajjatan kasar Iran da Suka rasa rayukan su a tirmitsitsin aikin hajjin 2015. Shekarar data biyo wannan kuma suka fille kan Sheikh Nimr al-Nimr, wani malamin Shia dan Saudi Arabiya mai tarin mabiya.  

Kazalika Saudi Arabiya ta yanke hulda da Iran ta kuma Jagoranci wani kawance na kasashe mabiya mazhabar Sunni. 

Bayan wadancan shekaru biyu, Yarima Muhammad wanda, tun watan yuni ya zama Yarima mai jiran gado, ga alamu ya fara Sabon tunani. Maimakon fito-na-fito da kasar Iran da mabiyan ta, ya fara jawo su jiki da sarakunan su. Ya sabunta dangantaka da Iraqi, Wadda basa ga maciji na tsawon shekaru 25, inda a wannan watan aka bude kan iyakoki ga mutane da kayan masarufi, Wadda ta kasance a rufe tun shekarar 1990. Ya kuma tura Shugaban maaikatan sa zuwa Bagadaza su rattaba hannu akan yarjejeniyar musayar bayanan sirri, kuma ya kawo tawagar cinikayya ta iraqi zuwa birnin Riyadh.

A watan yuni ya karbi bakuncin fara ministan Iraqi dan Shi’a, Haider al-abadi. A watan Yuli an hango shi yana fara’a a birnin Jiddah, tare da babban malamin Shi’a na Iraqi, Sayyid Muqtada al-Sadr.

“Masu tsaurin ra’ayin Sunni da masu tsaurin ra’ayin Shi’a basa gina kasashe ko Al’umma”, kamar yadda wani ministan Saudi Arabiya ya Rubuta a Shafin tweeter.

Gidan Sarautar Saudi na shirin bude karamin ofishin jakadanci a Najaf, wanda shine babban birnin Mabiya mazhabar Shi’a dake kudancin iraqi, kuma za’a samar da jigila daga Saudiyya zuwa birnin ga dubban yan Shia dake kasar domin ziyartar kabarin Sayyadi Ali.