An Tsare Wani Alhajin Nigeria Domin Ya Dauki Abin Tsintuwa A Harami.

Spread the love

Jamiā€™an tsaron Haramin Makka sun cafke wani Alhajin Nigeria da ya sunkuya ya dauki wani abin tsintuwa a harabar Haramin.
Da yake bayyanawa wakilin Muryar Amurka yadda abin ya faru, karamin jakadar Najeriya a Saudi Arabia, Alhaji Sani Yunusa yace akwai kyamarori fiye da dubu biyu a Masallacin da kewayen sa , wadanda ke nuna dukkan abinda ke faruwa a ciki da harabar masallacin.
Don haka Alhaji Yunusa ya shawarci
Alhazzai da su gujewa daukar duk wani abu da suka ga ya fadi a Haramin domin tsira da martabar su, kuma da gudun mummunar fahintar tsintuwar.


Haka kuma karamin jakadar ya zagaya gidajen Alhazan Najeriya domin yi musu wannan gargadin, yana cewa ta haka ne Alhazan na Nigeria zasu tsira da kimar su da martaban su.