Tashin Hankalin Da Musulunci Ya Shiga Bayan Harin 9/11

Spread the love

Daga : Aliyu Dahiru Aliyu

Tun bayan harin da Osama bin Laden ya kai wa tagwayen dogayen ginin Amurka da kuma hedkwatar tsaro ta Pentagon a ranar 11 ga watan Satumba na 2001, Musulunci bai kara shiga zaman lafiya ba.

Hoton Musulunci ya sauya daga zaman lafiya zuwa tashin hankali, daga kokarin cigaba zuwa kokarin cibaya. Yaki ya fara daga Afghanistan zuwa Iraq, daga Syria zuwa Libya, daga Yemen zuwa Rohingya, daga Somalia zuwa arewacin Nijeriya. Musulinci ya shiga yanayin da a tarihi bai taba shiga irinsa ba.

Hare-haren kunar bakin wake suka fara zuwa har kasashen turawa tun daga dan asalin Nijeriya, Umar Abdulmutallib, da aka kama a jihar Detroit a Amurka har zuwa harin da aka kai birnin Paris, bayan wanda dama mu mun saba gani tun daga Maiduguri har zuwa masallacin sarki dake Kano. Musulmi suka fara ganin tsangwama (Islamaphobia) kwatankwacin wacce yahudawa suka samu a shekarun baya (anti-semetism) da ta sanya Adolf Hitler ya yi musu kisan kiyashi a lokacin yakin duniya na biyu.

Ba na goyon bayan kowanne irin ta’addanci da sunan addini ko da sunan kishin kasa ko wata fahimta. Ba na tausayawa ‘yan ta’adda kamar yadda nasan ba tausayina suke yi ba. Daga abinda Zionists suke aikatawa ga miskinan Palasdinu a Isra’ila zuwa abinda mabiya addinin Buddha suke aikatawa miskinan Rohingya a Myanmar, ko abinda ‘yan ISIS suke a Syria da Iraq ko na ‘yan Boko Haram a Nijeriya ko kuma na ‘yan Alka’ida a Afghanistan; babu wanda nake goyon baya. Hatta abinda turawan Klu Klux Klan suke yi wa raunana bakar fata a Amurka, ba na goyon baya balle wanda Hitler ya yi wa yahudawan Jamus.

World Trade Centre attacks

 

Masu karfi ne suke kashe raunana kuma masu makami su kashe wadanda basu ji ba basu gani ba. Don haka rubutuna yana kokarin bayyana halin da Musulmi masu son zaman lafiya suka samu kansu daga bangaren masu yakarsu a cikin gida da kuma masu ganinsu a ‘yan ta’adda daga waje.

Kididdiga da lissafi sun riga sun nuna dama tun lokacin da George W. Bush ya fara abinda ya kira yaki da ta’addanci (war on terror), a kan Musulmi masu son zaman lafiya duk abin yake karewa. A cikin gida, ‘yan ta’addan da suke fakewa da jihadi suna kiransu munafukai yayin da daga waje kuma ana ganinsu suma yan ta’adda ne!

Kudin goron da aka yi wa Musulmi ya sa ake gani kowanne irin Musulmi a matsayin wani soja mai tafiya da bama-bamai a jiki da yake shirin tashin jama’a, musamman idan yana sanye da kayan larabawa ko kuma ya tara gemu. Caji ya yi yawa a filayen jirgi matukar sunanka ya yi kama da na Musulmi ko na larabawa. Rayuwa ta kara kuntata a gun Musulmi mai son zaman lafiya a ciki da wajen addininsa. Idan kana son zaman lafiya to, ka yi shigar turawa duk lokacin da za ka yi tafiya don kada wata shiga ta sanya a bata maka lokaci a filin jirgi.

Abu mafi muni shi ne, hatta kisan da ake yi ko na kai harin ta’addanci daga kungiyoyin ta’adda ko kuma na sojojin Amurka da kawayenta (NATO), duk a kan miskinan Musulmi masu son zaman lafiya yake karewa! Yayin da su masu da’awar jihadi da ma shi suke gani suna yankawa su kuma masu yaki da ‘yan ta’adda suna kuskuren ganinsa a dan ta’adda! Saboda illar da harin ta’addancin 9/11 ta sanya ba a mutunta ran Musulmi kuma ba a fiye tausaya masa ba.

A Kashmir, gwamnatin kasar Indiya na kashe Musulmi, amma ba a cewa komai saboda da ma Al’qaeda ta bata su. A Myanmar ana kashe ‘yan Rohingya, amma shi ma ba a magana, saboda ana ganinsu a ‘yan ta’adda kamar yadda Aung San Suu Kyi ta fada. Kafin wannan, an kashe Musulmi a Chechenya da karfin Rasha. An kashe Musulmi a Albaniya a karkashin Milosovich! Duka dai abinda daga Musulmi yake farawa ya kare a kan Musulmi.

Illar da harin 9/11 ya yi mana ta yi yawa kuma ita ce ta janyo har ake ganin ran mu ba a bakin komai ba. Lokaci ya yi da za mu nunawa duniya son zaman lafiyar addinin mu kamar yadda Annabin mu Muhammad (saw) ya koyar, don mu rage ganin wannan bala’i a cikin gida da kuma wajenta. Mu bi salon Mohatma Mohandis Gandhi ko Marthin Luther King wajen neman hakkin ba tare da zafafan kalamai ko neman zubar da jini ba. Ba laifi ba ne idan mun koyi wani abu a gun wadanda ba Musulmi ba, domin Manzon Allah Annabi Muhammad (saw) ya ce, hikima kayan mumini ce, duk inda ya ganta to, dauka yake yi.

Gaskiya za ta iya zuwa daga gun kowa, kuma za mu iya karbarta a duk inda muka ganta. Ko a gun Ahmad bn Hanbal, Ahmad Tijjani, Abdulkadir Jilani, Ibn Taimiyya ko Ahmad Ghulam. Za mu karbeta a gun Richard Dawkins, Lawrence Krauss ko Mussolini. Mu dai kawai mu nemar wa kan mu mafita daga halin da muke ciki a yanzu.

A yayin da ake ganin addinin mu a matsayin na tashin hankali da kashe-kashe, mu kuma za mu iya bayyana addinin mu a matsayin zaman lafiya da soyayya, kamar yadda aka koya mana a cikin addinin. Ta haka ne kawai za mu kubuta daga halin da muke ciki a yanzu na rauni tun bayan harin 9/11.

Twitter : @aliyussufiy