Hukumar Kustom Ta Bankado Bindigogi 1,100 Daga Kasar Turkiya

Spread the love

Hukumar hana fasa kauri ta kasa, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke jihar Legas, ta kama manyan bindigogi sama da dubu daya.

An da gano Wannan dila ta bindigogin ne wadanda aka kunshe su da sunan kayan bandaki da wasu kayan karau na wanke-wanke. Amma bayan tsananta bincike an gano bindigogi ne.

Shugaban hukumar kustom na kasakanar Hamid Ali mai ritaya, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar yau,indaYa kara da cewa an shigo da bindigogin ne daga kasar Turkiya.
Bindigogin sama da dubu 1 dai kamar yadda shugaban hukumar kostom ya bayyana, ko wacce daya tana iya hallaka mutane da dama a cikin lokaci guda ba kamar yadda sauran bindigogi suke ba.