Hisbah Ta Kame Mabarata 1,429 A Kano

Spread the love

Babu Maboya Ga Masu Bara A Titi

Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano ta kame masu bara 1,429 bisa karya dokar hana barace-barace a tituna, tsakanin watannin Janairu zuwa Augusta, kamar yadda wani jami’in hukumar, Mallam Dahiru Muhammad ya bayyana.

Muhammed, wanda shine yake kula da sashen hana bara na hukumar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa 420 daga cikin wadanda aka kama yara ne, yayin da 1,009 manya ne.

Bayanai a kan mabaratan ya nuna cewa 860 daga ciki sun fito daga Kano, yayin da 551 suka fito daga jihohin Jigawa, Kaduna, Katsina da Niger,inda 18 kuma daga jamhuriyar Chadi Suke.

Jamiā€™in yace tuni suka sallami wasu daga cikin mabaratan da suka karya dokar sau daya da kuma wadanda suke da tabin hankali.