Aung San Suu Kyi Ta fadi Dalilanta Na Kashe Musulmin kasarta

Spread the love

SHUGABAR KASAR Mianmar wato Burma
Aung San Suu Kyi Ta fadi dalilanta na kashe Musulmin kasarta, tare da tuhumar Musulman Duniya
Ta fara da mamakin yadda dukkan kungiyoyin musulmai suka hade mata kai suke zarginta da kisan Musulmai sama da dubu biyu cikin mako biyu, alhali suna kallon kasar Saudiyya ta kwashe shekaru tana luguden wuta akan al’ummar musulmi a kasar Yemen.
Mrs. Suu kyi tayi mamakin yadda Shugaban kasar Najeriya Buhari ya umarci Shugaban Askarawan Kasar wato Tukur Buratai ya aiwatar da kisan kiyashi akan Musulmi mabiya Mazhabar Shi’a, inda ya kashe sama da mutum dubu cikin kwana biyu.
Taci gaba da cewa yadda yan kasarta suke kashewa su kona haka suma sojojin Najeriya suka kashe suka kona suka tattara gawawwakin suka binne a rami guda, wanda tace ko ita batayi haka ba.
Ta kara da cewa mafiya yawan musulmai jinjinawa Buratai da Buhari sukayi akan wannan kisan. Ta kara da cewa “muna lura da abinda ke gudana a kafafen sadarwa na zamani inda mafiya yawan musulman kasar Musulmai mabiya Sunnah har da Malamai suka yabi Gwamnati akan wannan danyen aiki saboda yan shi’a ance sun tarewa Burtai hanya ne” ko a dokar Najeriya wanda yayi wannan laifin kashe shi akeyi a kona shi a rusa wurin ibadar sa?
Uwar gida Suu Kyi ta jefa tambayoyinta ga al’ummar musulmi kamar haka.
1- “Meyasa ni kadai za’a zarga baza’a zargi Buhari da Buratai ba tunda duk laifin iri daya ne?”
2- “Meyasa baza’a hana Sarakunan Saudiyya cigaba da kisan dasukeyi ba?”
3- “Meyasa Musulmai suka hade min kai ko don ni ba musulma bace?”
4- “Ku addinin ku haka ya koyar daku kuyita kashe kanku saboda banbancin fahimta”?
5- “Idan na bar addini na, na shiga Musulunchi nima baza ku zargeni ba don na kashe wadanda muke da sabanin ra’ayi dasu?
Kukan kurciya
Copied.