Dattawan Yarabawa Sun Yi Kira A Koma Kan Tsarin Tarayya Na Shekara Ta 1960

Spread the love

A wannan alhamis ne dattawan Yarabawa suka gama wani taro a Ibadan inda suka cimma matsaya na komawa kan tafarkin Tarayya Na ainihi, kamar yadda yake a jamhuriya ta farko.

Shugabannin Shiyyar Kudu maso Yammacin sun gamu ne a birnin Badin, inda suka yi kira Najeriya Ta amince da wani Kundin tsarin mulki irin wanda akayi amfani dashi tsakanin shekarun 1960-1963, kafin barkewar rikici a Najeriya wanda yayi sanadiyyar mulkin soja.

Wasu lawyoyi guda biyu Afe Babalola da Dr. Kunle Olajide sune suka fitar takardar bayan taron.

Sunce, kasar nan a matsayin ta na kasa mai yawan kabilu zata iya samun zaman lafiya ne da cigaba idan aka gudanarta akan tafarkin tarayya.

Suka ce kananan yankunan da suka hada tarayyar ko jihohi ne ko shiyyoyi suma dole ne a gudanar dasu akan tafarkin Kundin Tsarin Mulki wanda yake rubutacce, domin Magance zamba a kowane mataki kuma a basu yancin mallakar Arzikin su na maadanai, kuma a hannu guda zasu rinka bada gudunmawa ga Asusun Tarayya.

Sun Bada shawarar cewa kamata yayi Najeriya Ta kasance tarayya mai Larduna guda Shidda da kuma Babban Birnin Tarayya.

“Gwamnatin Tarayya zata shirya Dokoki ne kuma ta iya samun karfin iko akan alamura da aka ware a cikin sharuddan shirya doka dake cikin Kundin Tsarin Mulki na tarayya.

“kowane lardi kuma zai samu Kundin Tsarin Mulki nasa da zai ware Each region shall have its own constitution containing enumerated exclusive and
concurrent legislative lists regarding matters upon which the regions and the states may
act or legislate.

“Yankuna dake da takaddama ko kabilu suna da damar zaben wurin da suke shaawar zama ta hanyar zabe wanda ya sha banban da Jiha ko lardin da suke zaune a halin yanzu.

“Jihohi tare da lardin su, sune zasu tantance irin tanadin da zaa sanya a cikin kundin su na tsarin mulki domin gudanar da mulki.

“Sannan, akan bukata ta gamayya tsakanin jihohi akan tattalin Arziki da gine-gine, dukkanin irin wannan iko zai doru ne akan jihohi. ”

Takardar bayan taron ta bayyana cewa ikon kirkirar Jiha zai kasance a karkashin ikon Lardi ne, Wadda zai iya kirkirar jihohi matukar anyi kuriar raba gardama.

Hakan tace zai biyo bayan bukatar wani Kaso na Al’ummar wannan yanki ko Kabila, inda ita Kuma Jiha zata iya kirkirar karamar hukuma.

Taron ya cimma matsaya cewa jihohi suna da ikon sarrafa albarkatun da aka samu cikin yankunan su da duk Kudin shiga da suke samu.

“Za a raba Arzikin kasa ne da aka samu ta hanyar haraji, inda kashi 50 zai je ga jihohi, kashi 35 ga gwamnatin lardi sannan kashi 15 ga gwamnatin tarayya.

“A cikin tsawon shekaru 10 da fara aiki da Sabon kundin tsarin mulkin, za’a samar da wani asusu na bunkasa duk ma’adanai a cikin kasa.

(NAN)