Kilomita 135,000 Na Hanyoyin Najeriya Babu Kwalta

Spread the love

Darakta Janar na hukumar kula da harkokin gine-gine ta kasa, Mr Chidi Izuwah ya bayyana cewa akalla kimanin kilomita 135,000 na hanyoyin kasar nan ne basu da kwalta.

Daraktan yayi wannan bayani ne a birnin Abuja lokacin taron kungiyar injiniyoyi ta kasa na shekara shekara.

“Najeriya tana da kimanin hanyoyi masu tsawon kilomita 195,000, inda cikin wannan jimlar kilomita 32,000 na gwamnatin tarayya ne, kuma kilomita 31,000 na jihohi ne”.

“cikin wannan jimlar kilomita 60,000 ne kawai aka fidda su, kuma ko su din ma, da dama daga cikin su suna cikin mummunan hali saboda rashin kula da gyaran su.

Yace kudaden da Najeriya take kashewa akan harkokin hanyoyin Mota da layin dogo sunyi karanci sosai, kuma hakan ta jawo rashin ci gaban kasar, wanda shine ya haifar da rashin aikin yi da talauci.

Izuwah ya bada misali na hadin gwiwa da kamfanoni a kasar, musamman samar da wurin Aje kwantena a tsakanin Apapa – Lagos, wanda ya kawo raguwar cinkoso a tashin jirgin ruwa.

Hakan ta sanya raguwar Kudin jiran sauke kaya daga Dalar Amurka 525 zuwa Dala 75,inda hakan ya kawo wa Najeriya rashin Asarar Dalar Amurka Miliyan 200 a duk shekara.