Yadda Matashi Ya Gano Iyayensa Ta Shafin Facebook Bayan Shekaru 3 Da Bacewa

Spread the love

Facebook reunites mum with missing son after 3 years Habibu Umar Aminu, Katsina
Wani Matashi Mai kimanin shekaru 15, Mai Suna Sulaiman Ya samu haduwa da Iyayensa bayan shafewa shekaru uku yana gararamba sanadiyyar sace shi da wasu Barayin mutane sukayi a birnin Abuja.
Mahaifiyar Matashin, Hajiya Binta Umar ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa ta jima tana adduar neman Allah ya bayyana mata koda gawar dan nata ne, amma sai gashi Allah ya dawo dashi gaba daya.
Hajiya Binta tace wasu da ba’a San su ba sune suka dauke dan nata ranar Talata 6 ga watan Janairu, 2014, bayan tashin su daga makaranta a Abuja, inda yake a matsayin dan aji 4 na firamare a Kado.

Binta tace a wannan rana, na dawo gida kenan sai yata tace ai Suleman yau baya makaranta, kuma har yanzu bai zo gida ba.

“sai na tuntubi mahaifin sa, daga nan kuma sai aka fara bincike. Mun kai rahoto wajen yan sanda, munje asibitoci don dubawa ko yayi hadari ne, mun tuntubi yan uwa da abokai, amma duk babu labari” Inji Hajiya Binta.

Ganin babu wani labari sai aka rungumi addua, kuma muka hakikance cewa ya shiga hannun wasu da Allah ne kadai ya Sani. Mun kasance a cikin wannan ciwo har tsawon shekaru 3.

A cikin wadannan shekaru da iyalan ke cigiyar Sulaiman, sai aka nada Binta a matsayin Mai Baiwa Gwamnan Katsina, Aminu Masari Shawara akan Yara Mata. Hakan sai ya kara rura jita_jita cewa tayi amfani da danta ne wajen yin tsafi.

“Abin ya ban haushi, nayi tayin kuka. Daga nan sai na fara adduar Allah ya bayyana gaskiya, Inji Binta

Wata rana, a lokacin Binta taje Kaduna domin wani taro, tana cikin barci, sai wayar ta tayi kararrawa, sai karamin danta da suke tare ya tashe ta domin ta dauki wayar. Tana daukar wayar tace “abun mamaki sai naji muryar Sulaiman yana magana. Ina jin maganar na gane muryarsa, sai kawai na fasa kuka, shima sai ya fashe da kuka.

Daga nan Hajiya Binta ba tayi kasa a gwiwa ba sai ta wuce zuwa birnin Lagos inda Sulaiman yake.” Duk kamanninsa sun chanza, yanzu ya zama babban mutum, sannan yayi baki saboda wahala da ya shiga, Inji Binta

Sulaiman ya shiga mawuyacin hali bayan fitowa daga cikin gata zuwa rayuwa ta hannu baka hannu kwariya a birnin Lagos.

Sulaiman ya bayyana yadda wasu mutane da bai San su ba suka  kama shi, nan da nan sai hankalinsa ya gushe. “A lokacin da na dawo hankalina, sai kawai na tsinci kaina a kan Gawawwaki a gabar teku, wasu an yanke hannu wasu babu kai, sai hankalina ya tashi”. Sulaiman yace ya gane cewa yana Lagos ne bayan karanta wani rubutu a allon talla.

Sulaiman wanda ya kasance a dimauce sai ya rinka kwana a bakin teku yana shiga gari kullum don neman Abinci, inda yake aiki wajen masu saida Abinci da tura nakasassu a keke, inda a rana yake samun abun da bai wuce Naira 100 ba.

“A lokacin da nake zuwa gidan kallo, sai na gamu da wani Muhammad, kuma muka zama abokai, sai na koma matsugunin su. A nan ya hadu da wasu matasan dake daukar sa zuwa ayyukan birkilanci da sauransu.

“Koda yaushe na kasance Shiru bana magana, saboda haka mutane ke tsammanin ina da matsalar magana” Inji Suleman. Ya Kwashe shekaru biyu cikin wannan hali.

Wani Dare yana barci, sai Suleman yayi mafarki da Iyayensa, kuma da safe sai ya fara magana, inda ya bawa Muhammad da sauran mutane mamaki. Sai suka fara yi masa tambayoyi. “A nan na fada musu sunan iyayena, kuma sai suka bani shawarwari, inda wani ya ban shawarar na duba yan uwa na a facebook”.

Suleiman ya gano Shafin Facebook na mahaifiyarsa, kuma ya tura mata bukatar abota. “Ban samu amincewar ta ba, sai muka fara tuntubar abokanta, sai daya daga cikin yan uwa na ya amince da abota ta, sai muka fara tattaunawa, lokacin da na fada masa ko ni wanene sai ya fashe da dariya, yana tsammanin ni mai yaudara ne dake son cutar da su.

“Dan uwana sai ya turo min lambar mahaifiyata, wanda da itane na kirata a wannan daren, kuma mukayi magana, Inji Sulaiman.