YADDA GANDUJE YA KETA KWANKWASO A TARON BUHARI

Spread the love


Daga Bello Muhammad Sharada

Jama’ar da suka taru a shatale-talen Golden Jubilee daf da gidan gwamnatin jihar Kano a jiya Alhamis da rana, suna murna suna tafi sun amsa kiran la’antar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a karakashin jagorancin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

An yi taron siyasa ne domin nuna karin mubayi’a ga shugaban kasa BABA Buhari da aka baiwa Ganduje abin magana, ya lissafo siffofin Sanata Kwankwaso guda biyar:

Na farko ya ce Kwankwaso Bala’i ne
Na biyu Kwankwaso Annoba ne
Na uku Kwankwaso Shashasha ne
Na hudu Kwankwaso Sakarai ne
Na biyar Kwankwaso Munafiki Ne

Bayan ya gama lissafin siffofin sai kuma ya haska makomar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai gamu da ita

Na farko ba zai yi albarka ba
Na biyu za a la’ance shi
Na uku za a kore shi daga APC
Na hudu za a tsangwame shi a yi masa As ! as ! as ! a tura keyarsa gaba

A karshe ma dai Gwamna Ganduje ya aibata duk masu yin biyayya ga Sanata Rabiu Kwankwaso da cewa BAKAKEN BIRAI NE kuma KURAYE