Yadda Wata Mace Tayi Zaman Aure Da Maza Biyu

Spread the love

Wata Mata Mai suna Modinat Mufutau, ta bayyanawa Kotun Customary ta Idi-Ogungun dake Agodi a birnin Ibadan yadda take raba zaman aure ga Maza Biyu da take aure, domin bayan bukatar ta da kuma samun kudi.

Modinat dai ta bada wannan labari ne bayan da lamarin yayi tsami tsakanin ta da daya daga cikin mazan, Ajadi Mufutau,  inda ta je Kotu domin neman izinin sakin sa, bayan shafe shekaru 12 tare.

Ta fadawa Kotun cewa ta hadu da Mufutau ne a shekarar 2005, lokacin da har yayi mata ciki ba tare da anyi Aure ba.

Tace da farko dai ya nuna tamkar shi mutumin kirki ne.

“Amma bayan yi min ciki, sai ya fara wulakanta ni, har da duka idan na tambeyeshi Kudin zuwa Asibiti. To bayan na haihu sai kawai na watsar dashi na kama wani Mijinta, saheed, wanda shima bayan shekaru biyu yayi min ciki, amma bayan na haifi da na biyu sai ya maidani abar duka.

“Daga baya sai na koma wajen Mufutau, har na samu ciki na uku, to amma shima Saheed, wanda na haifar wa da na biyu, shima sai yace yana son mu cigaba.

“Daga nan sai na yanke shawarar zama da su biyun, kuma ban samu matsala ba har saida suka gamu a gidan da nake haya, kuma suka yi fada. ” Inji Modinat

“Ala Gafarta Mallam, yanzu na yanke shawarar sakin Mufutau, saboda ya daina bani kudi domin dawainiyar yaya biyu da na haifa masa, tun daga lokacin da sukayi fada da daya mijin nawa. Modinat ta fadawa Alkalin

Mufutau kuwa da yake maida martani a Kotu yace “Modinat mace ce Maras Kunya. Ban taba sanin cewa har yanzu tana hulda da Saheed ba, har sai da na ganshi a gidan da na kama mata haya, kuma bata dauki hakan a matsayin kuskure ba.