Masu Garkuwa Sun Sace Tsohon Minista A Najeriya

Spread the love

 

Rundunar yansanda A Jihar Nassarawa ta tabbatar da kame tsohon Ministan Kwadago, Mr Hussaini Akwanga.

Akwanga yayi aiki a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo, amma aka Tsige shi sanadiyyar wata badakala ta Naira Miliyan 214 na katin dan kasa.

Mai magana da yawun Rundunar yansanda ta Nasarawa, DSP Kennedy Idirisu, wanda ya tabbatar da lamarin yace wasu yan bindiga ne sukayi awon gaba da tsohon ministan a gonarsa dake Hanyar Wamba a garin Akwanga a ranar 22 ga watan Augusta.

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun dukufa wajen farautar masu Garkuwar.

A wani labarin kuma Iyalan Tsohon Ministan sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa masu garkuwar sun tuntube su, inda suka nemi wani jimlar kudi da baa bayyana ba.

A watan Mayu da ya gabata ma dai, masu Garkuwa Sun Sace Mahaifiya da yar uwar Dan Majalisar Jihar Nasarawa, Hon. Kassim Mohammed a garin Akwanga.