Indiya Ta Kawo Karshen Saki-Uku Na Aure A Lokaci Guda

Spread the love

 

A Yan shekarun nan bayan bullowar fasahar sadarwa ta zauren zumunta, Musulmi a kasar Indiya sukan saki matansu ta hanyoyin Facebook, whatsapp, ko ta hanyar skype.

Wannan dama idan aka hada ta da hukuncin saki uku a lokaci guda, ya bawa Maza damar yin saki ba tare da wani bata lokaci ba, inda hakan ya jawo cin zarafi da wulakanci ga mata.

Wannan ya sanya wasu mata tuhumar wannan matsayi a kotun koli ta kasar Indiya, inda alkalai uku suka rinjayi biyu, cikin alkalai biyar da suka kada kuria akan hana saki uku a lokaci guda.

“Mun shaidawa Kotu cewa wannan hukunci na saki uku a lokaci guda bashi da wani matsayi ko hujja a doka ko a cikin Kurani,” Inji Balaji Srinivasan, lawyan mai kara, Shayara Bano, Wadda Mijinta ya sake ta ta hanyar saki uku a takarda.

Jam’iyyar Bharatiya Janata mai mulkin kasar ta goyi bayan masu kara akan wannan lamari, inda fara ministan Narandra Modi ke yawaita kalubalantar wannan ta’ada.

“Ta bawa mata Musulmi yanci, kuma zata kara musu Kwarin gwiwa,” a wani sako da Modi ya aika ta tweeter, inda  yace hukuncin ya shiga Tarihi.