Mace Mai Farauta Zata Kamo Masu Garkuwa Da Mutane A Taraba

Spread the love

Wasu Mata Masu farauta a jihar Taraba Aisha Bakari da Habiba Husseini sun ci alwashin zakulo duk masu Garkuwa Da Mutane in gwamnatin jihar ta basu dama.

Masu farautar sun Bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a wata tattaunawa a birnin Jalingo.

Suka ce yaki da masu garkuwa da mutane ko yan ta’adda, ba wai yana bukatar karfine kawai ba da Makamai, yana bukatar Ilimi akan Lungunan da ake yakin da kuma irin mutane dake wurin.

Bakari, Wadda ta kira kanta “Sarauniyar Mafarautan Adamawa”, tace kawayenta dake surkukin yankunan Taraba a shirye suke su Ja daga domin chafko duk Barayin mutane a yankin, domin mika su ga jami’an tsaro.

“Abin da kawai muke bukata gwamnati ta zauna damu ta fitar da matsaya “, Inji Bakare.

Ta bada labarin yadda ta jagoranci matan mafarauta a yankin arewacin jihar Adamawa  wajen kakakin mayakan Boko Haram a yankin.

Tayi alkawarin amfani da irin wancen salon a jihar Taraba.

Bakari tace masu farauta sun samu gagarumar nasara a shekaru hudu da suka gabata a yake – yake a garuruwan Gombi da Maiha Da Madagali, inda tace yakin suma ya zo musu da asara inda suka rasa da dama daga mutanen su.

Tayi kira ga gwamnatoci a kowane mataki su tallafawa mafarauta da makamai da abun hawa domin basu kwarin gwiwar tunkarar yan ta’adda.

Itama abokiar aikin nata Hussaini tace da matan Taraba cikin gwagwarmayar yanta da dama daga cikin wadanda Barayin mutane suka kama.

“Muna bada bayanai masu amfani ga jami’an tsaro. Ina tabbatar maka zamu yi namijin kokari idan gwamnati ta bamu dama”.

Hussaini ta kira mata a jihar su yunkura su shiga kungiyar mafarauta, inda tace mata basu da kyakkyawan wakilci a yakin da akeyi da yan ta’adda.