Mace Ta Yiwa Mijinta Kulunboto Yana Jinin Al’ada

Spread the love

 

witchcraftwitchcraft

A wani lamari mai kama da Juju, magidanci mai shekaru 40, mai suna Chitungwiza yace ya shafe sati biyu yana fama da Jinin Al’ada irin na mata.

Magidancin ya bayyanawa jami’an tsaro yadda yake fama da ciwo idan yazo yin fitsari, sannan kuma yana zubda jini, lamarin da ya Zargi matarsa Sheila Kahari da yi masa tsafi.

“Dan uwa, ina cikin ciwo, in fada ma gaskiya, na shafe lokaci ina cin amanar matata, kuma ina kyautata zaton, itace tayi min tsafi ” inji Magidancin

“Da farko na dauka cutar tsagiya ce, amma ba haka bane, kuma zafin ya sanya ni dole na bayyana abin da nake yi a boye, inda muka tuntubi yan uwa har surukai na. Maganar da nake yanzu surukai na sunce sai na saya wa matar tawa jaki dan shekaru 15 a matsayin diyyar cin amanar matata.

“Matar tawa ta tilasta min in je wajen Boka Sekuru Banda, kuma ina tsammanin Sekuru Banda yana da hannu akan matsala ta.

“Bani da wani zabi, na ci amana kuma idan fallasawar da biyan diyyar itace mafita, a shirye nake na je wurin Sekuru Banda.

Sheilah ta ki yin magana da yan jarida inda ta gudu. Amma Boka Sekuru Banda ya tabbatar da cewa yana bawa matan aure taimako da ke sanya faruwar wani lamarin da zai sanya Magidanci ya koma ga iyalin sa.

“Kullum ina ganin mutane dake neman taimako akan Maza masu cin amana, wasu suna zuwa ne da daddare domin kada mazansu su gansu” inji Boka Banda

“Zan iya sanya maci amana yana yin wani abu kamar Jinin Al’ada, ko wani abu na alaurar mace ya fito masa ko yin magana da dabbobi, kawai domin ka koma wurin matarsa.