Da Gaskene Kuwa? An Haifi Jaririya Da Juna Biyu.

Spread the love

Newly born baby

(dpa/NAN) An Haifi Jaririya da juna biyu a kasar Indiya a wani lamari mai ban mamaki dake nuna cewa cikin ya kasance abokin tagwaitakar Jaririyar ne.

Mai Daukar Hoton Jikin Bil’Adama,  Bhavna Thorat tace tun yayin awon cikin aka gano akwai wani Dan kunshi da kasusuwa a cikin dan tayin da aka gani a watan Yuli.

“Yayin gwajin ciki, mun gano wani dantayin da kwakwalwa, kasada, da kafafuwa a cikin mahaifi dake cikin jaririyar. ”

“Uwar ta samu cikin tagwaye ne.  Amma sai daya ya shiga cikin daya, suka kuma dau tsawon sati 13 a haka.” Inji Thorat.

Bayan haihuwar jaririyar a ranar 20 ga watan Yuli a Asibitin Bilal dake Thane, kusa da yammacin birnin Mumbai, an gudanar ta tiyata domin cirewa daya jaririn.

Ka zalika wasu masu aikin fida a wata asibitin ne suka samu damar cirewa a ranar 25 ga Yuli, inda aka samu Namiji mai tsawon sinti mita 7 kuma mai nauyin 150 grammes.

Masana dai sun ce irin wadannan matsaloli guda 100 kawai aka iya ganowa a fadin duniya.