An Yiwa Mahajjacin Sokoto Fashi A Madina

Spread the love

Wani Mai aikin Hajji daga karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sokoto, Mallam Sani Musa ya fada hannun yan fashi a cikin birinin Madina.

Maniyyacin ya bayyana cewa an yi masa rufa-rufa ne aka sanyashi cikin wani lungu aka yimar kwace, bayan dawowarsa daga Masallacin Manzon Allah da daren Asabat.

Musa yace lamarin dai ya afku ne bayan da ya rasa yan uwansa da suka je masallaci tare, ganin ya dimauce sai wasu suka bullo da nufin taimaka masa domin ya gane masaukinsa.
Wanda ya tuntube shi domin taimaka masa ya nuna masa wata hanya ne, ashe duk bai sani ba wasu mutane biyu n biye dasu.
“koda na shiga wani lungu sai suka dakume ni suka sanyani cikin wata kwana suka tilastani na basu Kudi na na Guzuri”. Inji Musa
 
 Koda yake dai yace Yan fashin suna jin Hausa, amma bashi da tabbacin ko yan Najeriya ne.
Yanzu haka dai Musa ya samu tallafi daga yan uwansa wadanda sukayi masa karo-karo domin samun abin da zaina cin abinci. Malamin ya ja kunnen Maniyyata su rinka tafiya cikin ayari domin kaucewa irin wannan matsala.