Ko Kun San Yadda Fir’auna Ya Gina Dala A Masar? Kashi (1)

Spread the love

Babu Na’urar Daukar hoto kimanin Shekaru Dubu da suka gabata, lokacin da mutanen Masar na shekarun baya suka gina Dalar nan da ake kira Dalar Giza, ga kowane daya daga cikin Fir’aunoni uku wato Khufu, Khafre da Menkaure.

Domin haka masana Kimiyya suka dauki gabaren harhada hanyoyin da aka bi aka gina irin wadannan Manyan Gine-Gine. An share sama da shekaru 20 ana nazartar yadda wannan lamari ya kasance.

Dala ta farko wadda itace mafi girma a Giza, Fir’auna Khufu wanda yayi mulki a shekarun 2551 B.C shine ya gina ta. Wannan Dala tasa wadda ke da tsawon Kafa 455, itace ake kira “Babbar Dala” wadda a shekarun baya ake lissafata a cikin abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya.

Ita kuwa Dalar Khafre wanda yayi mulki a shekarun 2520 B.C, ta dan gaza ta Khufu ne da kadan. Mafi akasarin Masana na ganin wani hoton fuska da aka gina kusa da wannan dala, hoton Khafre ne, kuma shine ya gina shi. Fir’auna na Uku da ya gina Dala a Giza shine Menkaure, wanda yayi mulki a shekara ta 2490 B.C, wanda shine ya zabi gina karamar Dala da ke da tsayin kafa 215.

Fasahar da akayi amfani da ita wajen gina Dalar Giza an samar da ita ne a tsawon shekaru da dama, bayan fuskantar dukkanin wasu matsaloli da duk wani Masanin Kimiyyya ko Injiniya zai iya fuskanta a wannan zamani.

An samar da Dalar ne ta taswirar dakin Kabari wanda yake a kewaye da ake kira “Mastaba” a kasar Masar wadanda ake yi kimanin shekaru Dubu biyar  da suka gabata, kamar yadda wani masanin nazarin kayan tarihi Sir, Flinders Petrie ya bayyana. An samu babban ci gaba a lokacin Mulkin Fir’auna Djoser wanda yayi mulki a shekara ta 2630 B.C. An fara gina Dalar sa ne a Matsayin Mastaba bayan da daga bisani aka mata sukurwa shidda irin wadda ake yiwa Dalar. 

An dai dauki tsawon lokaci ana gini ana rushewa kafin a kai ga samun wannan taswira ta Dala da take a yanzu.

 

 

 

Zamu ci gaba da wannan labari a kashi na (2)

An fassara daga Live science.