Mansa Musa I: Mafi Kudi A Tarihin Duniya (2)

Spread the love

AYYUKAN ADDINI DA GINE GINE

A shekarun 1324 bayan dawowar Mansa Musa daga aikin Hajji a Kasar Makka, Ya jawo da dama daga cikin Masana na kasar Larabawa, Ma’aikatan Hukuma, da Masana zanen gidaje. A cikin wadanda ya dawo dasu kasar Mali akwai Masanin Taswirar Gidaje Ishaq El Teudjin wanda ya samar da Manyan Fasahohin gini ga kasar Mali. Ya zana gidaje da dama ga Sarki Mansa cikinsu har da Sabuwar Fadarsa da aka sawa suna Madagou, da Masallacin Gao, wanda shine gari na biyu a girma a kasar Mali, da kuma Sanannen Masallacin nan da har yanzu yana nan a garin Timbuktu, wanda shine gari mafi girma a Daular Mali. Wannan Masallacin ana kiransa Djinguereber. Mafi kayatarwar Zane da El Teudjin yayi shine Zauren Fadanci a Niani,  Babban Birnin Mali.

Aikin Hajji da Mansa Musa yayi ya bunkasa ilimin addinin Musulunci a Mali ta hanyar Masallatai, dakunan Karatu da Jami’o’i. Sanayyar sa a tsakanin manyan shugabannin Addinin Musulunci ya kara bunkasa cinikayya, Masana, Mawaka, da sauran masu fasaha, ta inda ya maida Timbuktu daya daga cikin manyan birane na Musulunci a Duniya, a daidai lokacin ta Musulunci ne yake tashe a dukkanin Manyan kasashe daga Spain zuwan tsakiyar kasar Indiya. Timbuktu tayi fice a matsayin Cibiyar Musulunci a daukacin Nahiyar Afirka.

Aikin Hajjin Mansa Musa shine ya jawo hankalin nahiyar Turai zuwa ga kasar Mali. Karni biyu na bayan tafiyarsa aikin Hajji masu tsara taswirar Duniya daga kasashen Italiya, Jamus da Spain suka fitar da taswira wadda ke dauke da kasar Mali, wadda kuma take nuna Mansa Musa. Irin wannan taswira ta fara fitowa a kasar Italiya a shekarar 1339 da sunan Musa da zanen hotonsa a jiki.

MATSAYIN DUKIYARSA A WANNAN ZAMANIN

Idan har aka yi lisssafi da yadda farashin kaya yake hawhawa, dukiyar Mansa Musa ta kai Dalar Amurka Miliyan Dubu 400.

 

Domin a wani nazari da wani shafin yanar gizo na  Celebrity Net Worth website, ya fitar, ya fitar da lissafin mutane mafiya Kudi a Tarihin Duniya su 24. Koda yake mutanen da aka ware sun fito ne a cikin nazari na shekaru Dubu, babu mace ko daya a ciki, kuma mutane uku ne kawai ke da rai a halin yanzu, inda 14 cikin mutanen 25 duk yan kasar Amurka ne.
Mansa Musa I shine mutum na farko da aka kiyasta dukiyarsa ta kai Dalar Amurka Miliyan Dubu 400, kuma ba’a taba samun wani mai dukiya da acikin wadannnan shekaru 1000 ya doshi samun irin wadannan makudan Arziki ba.
Sai Mutum na biyu wanda wani Iyali ne da ake kira Rothschild, wadanda har yanzu yan wannan zuri’a suna cikin mafiya tarin dukiya a fadin duniya. Wannan iyali sun tara dukiya da a yanzu akayi rabon gadonta, inda da dama daga cikin magadan suna cikin manyan masu kudi a sassa daban-daban. Wadannan Iyali suna da dukiyar da ta kai Dalar Amurka Miliyan Dubu 350.
Na uku kuma shine John D. Rockefeller, wanda a lokacin da ya mutu a shekarar 1937 yana da dukiya da takai Dalar Amurka Miliyan Dubu 340.

Idan akayi kwatance, talakan cikin wadannan mutane 25 shine Warren Buffett Mai shekaru 84 a duniya, wanda kafin ya fara bada dukiyarsa ga harkokin tallafi yana da Dalar Amurka Miliyan Dubu 64.

Wannan shine cikakkiyar Kididdigar Mutane ‘26 Mafiya Arziki A Duniya’:

1. Mansa Musa I, (Sarkin Mali, 1280-1331) $400 billion

2. Rothschild Family (Ma’aikatan Banki, 1740- ) $350 billion

3. John D Rockefeller (Masana’anta, 1839-1937) $340 billion

4. Andrew Carnegie (Masana’anta, 1835-1919) $310 billion

5. Tsar Nicholas II Na Russia (Basaraken Rasha Na karshe, 1868-1918) $300 billion

6. Osman Ali Khan, Asaf Jah VII (Mai mulki na Karshe a  Hyderabad, 1886-1967) $236 billion

7. William the Conqueror (Sarkin Ingila, 1028-1087) $229.5 billion

8. Muammar Gaddafi (Tsohon Shugaban Libya, 1942-2011) $200 billion

9. Henry Ford (Wanda ya kafa kamfanin mota na Ford, 1863-1947) $199 billion

10. Cornelius Vanderbilt (Masana’anta, 1794-1877) $185 billion

11. Alan Rufus (Sahabin William the Conqueror , 1040-1093) $178.65 billion

12. Bill Gates (Mai kamfanin Microsoft, 1955- ) $136 billion

13. William de Warenne, 1st Earl of Surrey (Bafade a Ingila, ??-1088) $146.13 billion

14. John Jacob Astor (Dan kasuwa, 1864-1912) $121 billion

15. Richard Fitzalan, 10th Earl of Arundel Bafade, 1306-1376) £118.6 billion

16. John of Gaunt (Dan  Edward III, 1330-1399) £110 billion

17. Stephen Girard (Mai Safarar Jirgin ruwa, 1750-1831) $105 billion

18. Alexander Turney Stewart (Mai Hannun Jari, 1803-1876) $90 billion

19. Henry, 1st Duke of Lancaster (Basarake a Ingila, 1310-1361) $85.1 billion

20. Friedrich Weyerhaeuser (Mai cinikin Katako, 1834-1914) $80 billion

21. Jay Gould (Mai gina hanyar dogo, 1836-1892) $71 billion

22. Carlos Slim (Dan kasuwa, 1940- ) $68 billion

23. Stephen Van Rensselaer (Mai gidan Haya, 1764- 1839) $68 billion

24. Marshall Field (Marshall Field & Company, 1834-1906) $66 billion

25. Sam Walton ( Mai kamafanin Walmart , 1918-1992) $65billion

26. Warren Buffett (Mai hannun Jari, 1930- ) $64billion