Mansa Musa Na Kasar Mali – Mai Kudin Da Babu Kamarsa A Tarihin Duniya (1)

Spread the love

Yadda Mansa Musa ya Shahara

Sarki Mansa Musa I ya samu mulkin kasar Mali ne ta wata hanya mai ban mamaki.

Karfin tafiyarsa aikin Hajji a Makka lokacin ba kasar Saudi Arabia bace, wanda ke mulkin Mali a wannan lokacin Abubakari II sai ya dora Musa ya yi masa riko a matsayin mukaddashin sa. Irin wannan mukami a wancan lokacin sanannen abu ne kamar dai mukamin mataimakin Shugaban kasar.

Irin wannan tsarin ya tafi daidai har zuwa lokacin da Abubakari yayi wani bulaguro zuwa gabar tekun atalantika, inda daga wannan tafiya bai dawo ba. Daga nan kawai sai Musa ya dare kujerar, tunda dai shi aka bawa jiran kasa.

Amma fa Musa ba haye yayi wa Sarautar ba, domin Kawunsa wanda ake kira Sundiata Keita shine ya kafa Daular Mali.

To kamar dai yadda da dama masana Tarihi zasu iya tabbatar wa, Musa ya tara duriyarsa ne ta hanyar fataucin zinare da gishiri, wadanda ke da tarin yawa a wancan lokacin a Afirka ta Yamma. Kuma yayi amfani da Kudin wajen gina cibiyoyin raya al’adu na kasar, musamman Timbuktu, wadda ya mamaye a shekarar 1324.

Mansa Munsa

A lokacin da Mansa Musa yaje aikin Hajjin sa zuwa Makka, to a nan ne fa aka fara sanin Karfin arzikinsa. Kasancewar yana da tarin dukiya da zai yi hidima da ita, tarin dabbobin dake cikin ayarinsa kawai, tun daga birnin Alkahira zuwa Madina zuwa Makka sun kai  60,000, da kuma tarin zinare.

Kuma Sun sayi abinci mai tarin yawa da har saida Saye – sayen ya jawo yar matsalar Tattalin Arziki na wani lokaci a duniya. Domin kuwa zinaren da yayi ciniki dashi ya kewaya duniya, yadda har yayi yawan da ya sanya darajarsa da karye.

A karshe dai ta kai ga Musa ya fara karbar rance a wurin masu bada bashi na birnin alqahira duk kuwa da yawan ruwa da suke chaza. Haka ta sanya Musa ya kasance shi kawai yana sarrafa farashin zinare a wannan yankin.

Dukiyar Mansa dai ta fita fili har zuwa wannan Zamani da muke ciki. Domin tarin Masallatai da Makarantu da ya gina har yanzu ana amfani da su, bayan kimanin shekaru 800.

Musa yayi mulki na tsawon shekaru 25, kuma ya mutu a shekarar 1325. A matsayin sa na Mai mulki da ya bunkasa ya sanya a zana taswirar kasar sa aka kuma sanya hotonsa a ciki,  wanda masu zanen taswirar duniya na kasar Italiya suka yi.

Map