Musulmi Ko Saudiyya – Waye Ke Da Hakkin Mallakar Masallatan Makka Da Madina?

Spread the love

An bude wani Sabon babi na cece-kuce akan hakkin mallakar gudanarwar Masallatan nan masu alfarma na Makka Da Madina, inda Saudi Arabia ke zargin Kasar Qatar da rura wannan wuta.

Sarakunan Saudiyyah dai suna zargin Qatar da kitsa batun neman a bawa musulmin duniya damar fada a ji akan gudanarwar Masallatan.

Duk da fadin Qatar cewa bata San wannan labari ba, Saudiyya ta tsaya kai da fata cewa kasar tana neman buga gangar yaki ne da Gidan Sarautar Saudi. Qatar tace ita dai tayi tsokaci ne akan irin wahalar da mahajjatanta zasu sha a wannan aikin hajjin, ganin yadda aka musu Kofar Rago a ranar 5 ga watan yuni yayin aikin Umrah.

Hakanne ya sanya Ministan Kasashen wajen Saudiyya Adel Al-jubair yayi hasashen Qatar tana neman mayar da Masallatan hannun Musulmin duniya, wadda yace hakan tamkar neman yaki ne.

Shi kuwa Ministan harkokin Kasashen Wajen Qatar,  Sheikh Mohammed bin Abdulrahman  yace babu wani jami’i daga kasar da yayi irin wannan kalami.

“mun gaji da maida martani akan labarai na kariya. Sheikh Muhammad ya fada ga Al Jazeera.

Qatar dai ta Zargi Saudiyya da Zargi Saudiyya da sanya Siyasa a cikin aikin hajjin, inda ta gabatar da wannan korafi gaban Jami’in majalisar dinkin duniya akan hakkin dan Adam da Addini.