Ahmad Baba(1556-1627) Shine Siffar Malamin Addinin Musulunci – Inji Shehu Danfodio

Spread the love

Ahmad Baba (1556- 1627) wanda ake yi wa lakabi da Abul-Abbas al-Timbukti al-Tukruri, daya ne daga cikin dubban almajiran da Tsangayar Sankore ta yaye su. Shi ne wanda Dr. Ibrahim Sulaiman ya ce: Shehu Usman Dan Fodio ya kalle shi a matsayin cikakken hoto na yadda ya kamata ace malamin addini ya kasace a tsakanin al’umma.

A matakin farko ya yi karatun ilimin addini har ya kai magaryar tukewa a cikin dukkanin fannonin da ake da su a wancan zamanin, sannan ya zama mai shiryar da al’umma a cikin bangarori mabanbanta, ya kuma zama mai yi wa dukkanin mutane hidima. Abin koyi na gaba daga Ahmad Baba wanda shehu Usman ( r.a) ya gani, shi ne yin tsayin daka wajen kare manufofin al’umma da hana cin zarafin abubuwa masu kima na al’umma ( social Values) da akidunta da kuma cibiyoyoyinta. Ta haka ne, malamin addini ya ke zama garkuwa na halayen kwarai da al’umma ta ke da su, da kuma tsarkinta da kuma mutunta cin gashin kai nata. Kuma shehu ya kalli Ahamd Baba a matsayin mai kare hakkin talakawa da wadanda ake zalunta da kuma taimaka musu su cimma manufofinsu.

Nauyi na hudu da ya hau kan malami wanda Ahmad Baba ya ke a matsayin hotonsa , shi ne kare al’ummarsa da ganin cewa ta ci gaba da yin biyayya ga Allah da aiki da dokokinsa. Mataki na karshe wanda shi ma Shehu ya gani a matsayin abin koyi daga wannan malamin shi ne yi wa almajirai maza da mata tarbiyya wadanda za su ci gaba da shiryar da al’umma idan alamomin badala da lalacewa sun fara bayyana acikinta.

Idan ana yi wa birnin katsina kirari da sunan daya daga cikin fitattun malaman da ta samar da cewa: “Tudu Garin Dan Marina” to Dr. Ibrahim sulaiman ya samowa Tambutu kwatankwacinsa da shi ne Ahmad Baba da ya baiwa lakabin (Ruhin Tambutu). Kuma daidai ya ke da yadda Wali Dan Marina ya bayyana matsayin ilminsa da kansa acikin wasu rubutattun baitocin wakensa da cewa:

(Kullu ilmin zuqtuhu mil’ani, Summa jalastu jalsata-s-shib’ani.)
“Na dandani kowane ilimi har cikina ya cika.”
Sannan na yi zama irin na wanda ya koshi.”

Littatafan da Ahmad Baba ya rubuta sun haura arba’in a cikin fagagen dokoki (fikhu) da ilimin hadisi( Ilmul-Hadith) da tarihin fitattun malamai da siyasa da mandiki (logic).

Abu Abdullah Muhammad Ibn Ya’kub, marubucin littafin tarihin malaman moroko mai taken: “Al-Fihrisah” wanda kuma almajrin Ahamd Baba ne, ya bayyana shi da cewa: “Dan’uwanmu Ahmad Baba yana daga cikin masana, malamin fikihu kuma mai cikakkiyar fahimta. Kuma mawallafi ne wanda ya rubuta littatafai masu yawa kuma masu amfani. Sun kuma kunshi nazari na aqali da kuma naqali.

Ilimomin aqali, suna nufin wadanda ba na addini ba kai tsaye suna kuma bukatuwa da zurfin tunani da kuma kirkira, kamar mandiqi da lissafi da ilimin taurari da sauransu. Wannan yana tabbatar da cewa, tsangayar Tambutu ba ilimin naqali kamar kur’ani da hadisi da fikihu da usulu kadai ta ke koyarwar ba.

A cikin littafinsa na tarihin malamai mai taken: ( Kifayatul-muhtaj) , Ahmad Baba ya ambaci tarihinsa da na karatunsa. A ciki ya ce, ya yi karatun mandiqi a hannun mahaifinsa.

Dangane da Ahmad ne Sa’adi a cikin littafinsa na Tarikh-Sudan da ya ke ambaton malaman Tambutu ya ke cewa:

“ Daga cikinsu da akwai malamin fikhu masani mai yawan sani, wanda ba shi da tamka a zamaninsa, kwararre a cikin dukkanin fannonin ilimi, Abul-Abbas Ahamd Baba…. Ya sha kan dukkanin tsaransa, babu wanda ya ke iya tattaunawa ta ilimi da shi sai malamansa… mai mika kai ne ga gaskiya koda kuwa daga mutanen da su ke koma-baya ne a cikin al’umma, kuma baya yin sassauci akan gaskiya, koda kuwa a gaban shugabbanni ne da masu mulki”

Bayan karatun addini da dukkanin rassansa, Ahmad Baba ya shiga cikin tarihi a matsayin dan gwagwarmayar kare ‘yancin mutanen Afirka a lokacin da ake kamo su a matsayin bayi. Da akwai jan hankali a cikin sunan da ya baiwa littafinsa mai taken: “Jalbul-Ni-Imah Wa Daf’ul-Niqmah Bi Mujanibatu al-Zalamah Ulil-zalama”
Idan za a yi fassara ta kai tsaye ma’anarsa shi ne “jawo ni’ima da kuma kore bala’i ta hanyar nesantar azzalumai masu cuta.” Yana kuma Magana ne akan yadda ‘yan siyasa masu mulki su ke kamo musulmi a matsayin bayi suna sayar da su. Ya kafa kwararan dalilai daga nassi na addini akan haramcin haka. Kuma ginshikin nazariyya (Paradigm) wacce ya gina bayanansa akai ita ce cewa:” Dukkanin mutane ‘yantattu ne, a cikin wani kayyadajjen yanayi ne kadai su ke iya zama bayi.”

Mutanen da ya ke bai wa kariya anan, su ne na Borno da kuma kasar Hausa da su ka hada da kano.

Muhimman littafai guda uku da ya rubuta akan tarihin rayuwar malamai, mafi yawancinsu na Afrika da ya rayu da su da kuma wadanda su ka gabace shi su ne:

1-Naylul Ibtihaj Bi Tatrizil-Dibaj,

2- Kifayatul-muhtaj Li ma’arifati Man Laisa fil-dibaj,

3-Zayl Alal Kifayah

Sauran littatafansa sun shafi fikihu da ilimin hadisi da madiki da manhajar koyarwa da sauran fagage masu yawa.

Littafinsa na tarihin Muhammad Abdulkarim al-maghili, wanda aka fassara shi zuwa faransanci a 1855 yana daga cikin muhimman madogarar manazarta turawa a lokacin da su ke kokarin fahimtar yadda Afirka ta ci gaba ta fuskar dokoki.

Ahamd Baba ba haye ya yi wa malunta ba. Danginsa da aka fi sani da ‘Zuriyar Aqit” su ne masu samarwa Tambutu da sauran garuruwan Daular Sanghai alkalai da limamai na tsawon karni biyu a jere. Mahaifinsa shi ne malaminsa na farko wanda ya koya da shi mandiki kamar yadda mu ka gani a sama. Kuma a cikin littafinsa mai taken (Zayl) ya yi cikakken bayanin kakanninsa malamai da cewa:

“Ahmad Bin Umar Bin Muhammad al-aqit al-Tinbukti, kakana na wurin uba, ana kiransa da Alhaji Ahamd.Msanin fikihu ne da lugga da Nahwu da arudh ( ilimin waka). A tsawon rayuwarsa ya maida hankali akan ilimi. Ya kuma rubuta littatafai masu yawa, kuma masu amfani da hannunsa. Ya kuma mutu ya bar littatafai guda dari bakwai wadanda ya gaje su daga kakansa na wurin uwa, masanin fikihu And Agh Muhammad, da kuma kawunsa masanin fikihu da nahwu, Mukhtar. Ya yi aikin Haji kuma ya hadu da Suyudi da Khalid al-waqqad na jami’ar Azhar wanda limami ne ( farfesa) akan Nahwu.”

A cikin wannan littafin kuma ya bada labarin wani kawunsa:
“Abubakar Dan Ahmad Dan Umar Dan Muhamad Aqit. Haifaffen Tumbuktu ne wanda kuma ya zauni Madina. Kawuna ne. Mai zuhudu ne da gudun duniya. Mai yawan alheri ne da yawan sadaka, duk da cewa yana da karancin abin duniya. A wurinsa na fara yin karatun Nahwu. Yayi rubuce-rubuce da su ka kunshi nasihohi da sufanci.”

Daga cikin dangin Ahmad Baba ne alkali Aqib Ibn Mahmud Ibn Umar Aqit ya fito. Shi ne wanda marubucin “Tarikh al-Fattush” acikin babi na goma sha biyu ya bayyana da cewa:

“Shi ne mafi girman adalci da ijtihadi a tsakanin alkalan da Tambutu ta yi, wanda kuma ba a taba samun kwatankwacinsa gabaninsa ba, haka nan kuma a bayansa ba a sami daidai da shi ba. Ba kuma za a yi ba har abada!”!

Assa’adi, a cikin littafin Tarikh Sudan, a karkashin babi na tara da ya ke ambaton malaman Tambuku da salihan bayinta, ya bayyana wannan alkalin da cewa: “ Shi ne wanda ya cika kasarsa da adalci ta yadda ba a sami kwatankwacinsa a ko’ina ba.”

Ahmad Baba acikin littafinsa Naylul-Ibtihaj, da ya kunshi tarihin malaman musulunci na cikin Afrika da wajenta, ya bayyana wannan alkakin da cewa: “Mai tsayin daka ne akan gaskiya, baya tsoron zargin mai zargi akan tafarkin Allah. Mai shigewa gaba ne wajen yin ayyuka masu wahala da waninsa ya ke kasawa. Yana da karfin guiwa kalubalantar sarki da wanda ya ke kasansa- sarkin. Masu mulki suna kaskantar da kai a gabansa acikin duk abinda ya ke so. Idan kuma ya ga an yi wani abu da baya so, to zai cire kansa daga alkalanci ya shige gida ya rufe kofa har sai sun shawo kansa.”

• Alkali a karkashin tsarin Daular Sanghai yana a matsayin jami’in tafiyar da mulki ne, baya ga ayyukan shari’a da raba husumomi tsakanin mutane. Kuma tare da cewa sarki daga cikin zuriyar Askiyawa ne ya ke nada alkali a cikin garuruwa, sai dai duk da haka, yana cin gashin kansa ne. masu iko ba su tsoma masa baki a cikin ayyukansa.

Malaman Tambutu ba malaman fada ba ne ko masu banbadanci ga masu mulki. Malamai da alkalai ba su zuwa fada sai dai fada ta same su., idan ba wata lalura ba.

Mahmud Ka’ati, a cikin littafinsa na Tarikh-Fattush” ya ambaci cewa Sarkin Daular Sanghai mafi girma a tarihinta, Asikya Muhammad ( Askia The Great). Ya aike da fadawansa su yi masa wani aiki a cikin birnin Tambutu. Alkali Mahmud Bin Umar Bin Muhammad Aqit,ya hana a yi wa sarki wannan aikin, ya kuma kori fadawan daga cikin ganuwa. Sarki Askiya ya yo tattaki da kansa ya rabu da fadawansa ya koma wani wuri nesa da jama’a ya tsaya shi kadai. Ya aikewa da alkali dan sako akan cewa su yi mahada. Bayan haduwarsu ya yi wa alkali tambayoyi akan dalilin da ya hana fadawansa su yi aikin da ta turo su da shi. A karshe alkali ya yi wa sarki tuni da cewa a baya ya zo har gida ya same shi, ya roke shi akan idan ya ga yana aikata wani abu da zai iya kai shi ga shiga wutar jahannama, to ya shiga tsakaninsa da wuta.! Lokacin sai sarki ya tuno, ya kuwa yi wa alkali godiya.

Duk da cewa marubucin littafin bai amabci abinda sarkin ya so aikatawa, sai dai daga jawabin alkali Mahmud za a iya fahimtar cewa wani abu ne da ya kaucewa shari’a, saboda haka ya hane shi.

• Anan muna magana ne akan Sarki Askiya ( Askia the Great) wanda ya ci katsina da Zamfara da Zazzau da yaki ya kuma kashe sarakunansu. Ya kuma dorawa masarautar kano haraji na sulusin kudin shigrarta.

Wannan kadai, yana a matsayin manuniya da girman ruhin malaman Tambutu. Baya ga gudunmawar da su ka bayar ta fuskar ilimin addini.