Trojan Mutanen Dake Rayuwa Da Matattu

Spread the love

Cikin al’adu da yawa, idan mutum ya mutu ana binneshi ne cikin yan kwanaki da mutuwarsa, amma abin ya sha banban ga mutanen Trojan na kasar Indonesia. ┬áDomin su sukan rayu ne wuri daya da Gawawwakin.

Su kan warewa Gawawwaki dakunansu, kuma sukan yi musu wanka su chanza musu kaya. Wani lokacin ana aje musu Abinci har da sigari sau biyu a rana. Ana ajiye musu wata roba a cikin dakin da zata kasance kamar magewayi.

Galibi suna yiwa mamata allura ne da ake kira fornulin domin adana gawa kar ta rube.

Su kan dauki tsawon shekaru 12 ko sama da haka suna ajiye da matattu a cikin daki. “idan muka binnasu da zarar sun mutu to zamu ji damuwa cikin Gaggawa. Inji Mamak Lisa.

Ms Lisa ta kan bayyana mutuwar babanta a matsayin rashin lafiya,

bbc-living-dead-1.jpg
Wannan al’ada ta kabilar Trojan ta Kwashe karni da dama ana Yantandu. Ga akidar wasu da ake kira animist, kowane abu yana da rai, sai dai layin dake tsakanin duniya da lahira ba a iya gane shi.