Wani Dillali Ya Yiwa Bill Gates (Mai Kudin Duniya) Fintinkau A Tarin Dukiya

Spread the love

Jeff Bezos Ya Zama Mafi Kudi A Duniya

Jeff BezosĀ 

Dillalin sayar da kaya wanda ya kirkiro kasuwar internet ta Amazon Jeff Bezos yanzu shine wanda ya Fi kowa kudi a duniya, mukamin da Bill Gates yake kai a shekarar data gabata.

An hakaito cewa Jeff a yanzu yana da tarin kudi har Dalar Amurka Miliyan Dubu 90 da Miliyan 600 yayin da Bill Gates kuwa ya mallaki Dala Miliyan dubu 90 da Miliyan 100.

Kididdigar ta nuna cewa Jeff ya zarce Gates da Miliyan 500.

Kafafen Yada labarai dai ba zasu iya tantancewa hakikanin tarin dukiya da wadannan attajirai suka tara sai dai hasashe kawai.

Binciken da Jaridar Forbes ta fitar yanzu ya nuna yadda Bill Gates ya sadaukar da Dala Miliyan dubu 31 a Shekara data gabata domin taimakon jin kai.