“Mwila” – Kabilar Da Bata Cin Nama

Spread the love

Kabilar Mwila dake zaune a kudancin kasar Angola na daya daga cikin kabilun dake rayuwa akan al’adunsu a tsawon shekaru sama da dubu daya.

Wadannan mutane dake da siffa data sha banban da mafi akasarin makiyaya, suna harkokin noma ne da kiwo gami da neman Zuma.

Duk da cewa suna kiwo, amma al’adarsu shine basa cin nama sai dai kwai ko naman kaza da sauran ganyayyaki. Suna da kwalliya irin tasu da tayi kama da ta Masai na kasar Kenya sai dai tarin sarkar da suke sawa a wuyansu yafi na Masai yawa.

Mumuguila
Asalin Mwila dai sun fito ne daga cikin kabilar Bantu dake kasar Afirka ta Kudu, wadanda bayan babbar Hijira ta shekarun 1700 Mwila suka bar yankin na Afirka ta kudu suka koma yankin kudancin Angola.

Matan  Mumuhuila a kasuwar Mucuma, Angola

Rayuwarsu tana da dan tsauri, inda mata kan yi tafiyar kilomita 50 kafin su isa kasuwar Huila domin sayar da kayan su. Sukan yi ciniki ne na ban gishiri in baka manda. Domin basa amfani da wani kudi da ya wuce kayan Amfanin gona da dabbobinsu.

                                 Yan Matan Mwila a Birni

 

Sarauniyar kyau daga kabilar Mumuhuila

Kabilar  Mwila basa fadin sunayen mutane a bainar Jama’a. Wannan wani babban laifi ne.


Matan  Mwila, Angola

Matan Sukan lullube gashin kansu da wata jar kasa da ake kira Oncula, wanda ake yi ta hanyar nika duwatsu.  Su kan kwaba kasar da mai da busasshen bawon bishiya da busasshen kashin saniya.

Kitson Mumuila

Askewa gaban goshi alama ce Ta kyau.

Kwalliyar gashi dake sauka a wuyansu sunanta Nontombi, kuma tana da ma’anarta. Domin duk mata suna da nontombi 4-6, amma idan mace tayi uku to alamu ne na nayi mutuwa a danginsu.

 

Mwila


Muhuila woman between Mucuma and caiend

Mwila
Mwila woman carrying baby
Mwila girl of Jau tribe