Majalisar Wakilan Najeriya Ta Shiga Rudani Akan Gyara Kundin Tsarin Mulki

Spread the love

Hayaniya Ta Kaure Akan Gyaran Kundin Tsarin Mulki

 

Dogara

A wannan alhamis ne Majalisar Wakilai Ta Najeriya Ta fara tattaunawa akan rahoton wani kwamatinta na musamman akan gyaran Kundin Tsarin Mulki kasa na 1999.

Kudirin dokar gyaran wanda ya kunshi gyare-gyare 32 an gabatar dashi ne gaban zauren.

Majalisar Ta shiga yamutsi ne lokacin da wani Dan Majalisa Mojeed Alabi daga APC Jihar Osun ya Ja hankali akan doka majalisar inda yake neman a tattauna akan Rahoton sashe zuwa sashe kafin amincewa.

Dan majalisar ya kafa hujja da dokar majalisar ta 9 2(1) wadda take neman sai nayi muhawara kafin amincewa da kudirin.

Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ya ki amincewa da shawarar, inda yace tuni an tattauna akan sassan tun gabanin mika shi ga kwamatin.

An dai shafe mintuna 30 ana takaddama tsakanin Alabi da Dogara akan wannan batu kafin daga bisani yan majalisar suka rarrasheshi.