Yadda Miliyan 700 Ta Shiga Aljihun Hadimin Sarkin Musulmi

Spread the love

Why we bought N700m residence for Sultan in Abuja – Sokoto govt

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta fito ta bayyana masaniyar ta akan tsabar kudi Naira Miliyan 700 da EFCC take tuhumar wani na hannun damar Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Mai baiwa Gwamnan Jihar Sakkwato shawara akan jarida Alhaji Imam Imam shine ya fito yayi watsi da rade radin da akeyi na hannun Sarkin Musulmi a kan wannan kudade da suka shiga asusun Sarkin Fadan Sakkwato, Alhaji Kabiru Tafida. Imamu Imamu yace wancan kudi da ake zargi an ware su ne domin ginawa Mai Alfarma Sarkin Musulmi H karafaren gida na wannan jimla a birnin Abuja.

Mai Baiwa Gwamnan Shawara yace kuma wadannan kudaden suna cikin kwarya kwaryar kasafin kudin Jihar na shekara ta 2016, kuma akwai sahalewar Majalisar zartaswa akan lamarin.

Hukumar EFCC dai tana neman hujja ne akan yadda kudaden suka yi sabi zarce zuwa cikin asusun Kabiru Tafida wanda shine na hannun daman mai alfarma Sarkin Musulmi.

Mashawarcin gwamnan yace majalisar zartaswa ta jihar Sakkwato a yarjejeniyarta mai lamba CC (2016) 5R ta ranar laraba 28 ga watan Disamba 2016 ta amince da sayen ofishin da kuma gidan a birnin Abuja.