Sarkin Musulmi Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

Spread the love

Hukumar EFCC na binciken jerin harkallar zunzurutun kudade Naira Miliyan 700 daga asusun gwamnatin jihar Sakkwato zuwa asusun Kabiru Tafida, babban hadimin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Majiyar jaridar DAILY NIGERIAN daga hukumar EFCC sun shaida cewa, Tafida wanda shine mai rike da mukamin Sarkin Fadan Sakkwato ya shiga hannun hukumar kafin daga bisani aka bayar da belinsa ranar Talata.

Tafida ya bayyana cewa, wannan kudade gida za a sayawa Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad a birnin tarayya Abuja. Sai dai mai magana da yawun Gwamnan jihar Sakkwato Imam Imam ya shaida cewa, an sanya kudaden ne a kasafin kudin jihar, ta hanyar bin tsarin doka da oda.