Kasar Indiya Ce Ke Kan Gaba A Auren Kananan Yara

Spread the love

Child marriage in India

(Xinhua/NAN) Kasar India ce ke aurar da yara kimanin Miliyan 85 cikin Miliyan 103 na auren Yara da akeyi A Fadin Duniya.

Wani rahoto da wata Kungiya mai zaman kanta ActionAid India ta fitar Ya nuna cewa akan aurar da yara Dake kasa da shekaru 18.

Rahoton mai lakabin “kawar da Auren Yara A Indiya” yayi amfani da alkaluma ne dake cikin kididdiga ta yawan jama’ar kasar na shekara ta 2011. Alkaluman sun nuna cewa ana samun auren yara 150 a duk awa guda a kasar.

Yawan auren yaran da akeyi ya zarce yawan mutane dake kasar philippines, wadda itace kasa ta 12 a yawan mutane a duniya. Rahoton yace kashi 30.2 cikin 100 na daukacin matan da ake aurar wa a India.

Su dai mutanen Indiya suna ganin auren yarinya kafin a kawar mata budurci zai taimaka wajen kare martabar gidan su.