TA FARDEWA SAURAYIN TA CIKI DA ALMAKASHI

Spread the love

Wata budurwa ta fardewa sauratin ta ciki da almakashi a unguwar Kurna dake jihar Kano.

Wasu rahotanni sunce ta fusata ne tun lokacin da ya kaurace mata a lokacin da sallah ta karato, sai a yanzu ne da sallar ta wuce ya takura mata da aike zuwa gidan su don ta fito tadi wurin sa.

Saidata kwashe kwanaki bata fitowa, amma duk da hakan saurayin ya like mata, lamarin da yasa yana dawowa ta dauki almakashi ta zaburo kofar gida, tana isowa inda yake takai masa suka, kana daga bisani bayan da almakashin ya shige sai ta kara ja ta farde masa ciki.

Jim kadan da faruwar hakan ne wasu da lamarin ya faru akan idanun su, suka kwasheshi zuwa asibiti, sai dai kwanan sa daya acan ya rasa ransa ransa.

Dama dai ba wannan ne karon farko da ake zargin cewa samari kan guji yan matan su a lokacin da Sallah ta karato don gudun yi musu hidindimun sallah ba.