Kudan Zuma Ta Sa Wani Barawon Mota Mika Kansa Ga ‘Yan Sanda

Spread the love

A ranar Litinin din da ta gabata ne wani barawon mota ya fada ofishin ‘yan sanda a guje tare da mika kansa a matsayin barawo bayan da kudar zuma ta yi masa caa tana harbinsa babu ji babu gani

Wannan lamari dai ya faru ne a kasar Kenya,
inda wani mutum mai matsaikacin shekaru kuma dan asalin kasar Uganda mai suna Francis Sikadigu ya yi amfani da kwayoyin da ke fitar da mutum daga hayyacinsa wajen sace shi, shi da motarsa zuwa wani waje inda a nan ne ya sace motar

Bayan sace motar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sa mai motar ya kai kukansa wajen wani boka, inda boka ya dauki gabarar hukunta barawon har da ya sa shi ya dawo da motar

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Bungoma, Mista Kirui ya tabbatar da wannnan labarai inda ya ke cewa

“Abinda ya faru ba komai ba ne face maita kiri-kiri”.
“Za mu mika wanda ake zargi zuwa kotu da zarar mun kammala bincikenmu

Shi kuma Mai motar, Mista John Wafula, wanda sanannen mai hayar motoci ne ya bayyana cewa “Barawo Sikadigu ya zo wajen don na bashi hayar mota ta na tsawon kwanaki uku a ranar Juma’ar da ta gabata, muna cikin tattauna farashinne sai na dan bar wajen, inda a nan ne ya samu dama ya jefa wata kwaya a cikin abin shana.
“Kawai sai farfadowa na yi na ganni a babban asibitin garin Bungoma County”

Mista Wafula ya ci gaba dacewa “Bayan na kai rahoto gurin ‘yan sanda, sai na wuce wajen wani boka don a yi min aiki mota ta ta fito”

“Ina godiya ga ubangiji da ya dawo min da mota ta kuma aka kama barawon.

Ina son hukuma ta gurfanar da shi a gaban kotu don ya zama darasi a gare shi da sauran mutane”

Yan sanda sun nemi Wafula da ya kai su ga bokansa don ya sa kudar zuman da ta yanyame Sikadigu da ta bar jikinsa kuma sun yi nasarar samun boka Siraba Musali da aka bisani da Dakta Nyuki a rukunin gidaje na Marell, inda bayan ya yi ‘yan kulumbotonsa ne sai zumar ta bar bin Sikadigu, kuma ‘yan sanda suka koma da shi ofishinsu don ci gaba dabincike