Wani Barawo yayi Jinginar Yaro Dan Shekara 10 Akan Buhu 3 Na shinkafa

Spread the love

A wani lamari mai kama da zamba, wani mutum ya saci yaro dan shekaru 10 a kan titi ya yi musayar sa da buhun shinkafa 3 a wani shagon sayar da kayan masarufi a yankin Ijegun da ke jahar Lagos. Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya samu yaron ne yayin da yake kan hanyar zuwa sayo wa mahaifiyar shi man gyada, inda ya yaudare shi da cewar shi dan uwan mahaifiyar sa ne, har ya raka shi sayen man gyadan. Daga bisani, mutumin wanda ba’a bayyana sunan shi ba, ya dauki yaron zuwa wani shagon da ake sayar da buhuhunan shinkafa, ya nuna cewa tare suke da yaron, wanda ya kira shi da kanin shi. Yarinya mai jiran shagon mai suna Deborah ta fadawa Jaridar Vanguard yadda Mutumin ya karbi buhuhunan shinkafa guda 3 ya bar yaron a gurin ta da zummar zai je yacdawo da kudaden. Ta ce ta yi jiran duniya ba ta ga mutumin ba har na tsahon awa daya wanda a lokacin ne ta bukaci yaron ya kaita wajen mahaifiyar shi. Yaro kuwa yace mahaifiyar shi ba ita ya sayawa shinkafa ba, hasali ma a kan titi ya hadu da wannan mutumi.

A bangare guda kuwa iyayen yaro sun shiga rudani bayan da suka yi ta jiran yaron ya dawo daga aike ba su gan shi ba kuma tuni suka bazama nema. Lamarin ya tabarbare da suka je shagon da ake sayar daman gyadan aka fada masu cewa anga yaron tare da wani mutum. Lamarin dai yanzu haka yana wajen ‘yan sanda. Rahotanni sun bayyana cewa duk da ‘yan sanda sun baiwa iyayen yaron dan su, masu shagon sun tire akan sai an biya su kudaden shinkafar su. Yanzu haka dai ‘yan sanda na kan neman mutumin yayin da suke yunkurin sasanta masu shago da iyayen yaron.