Sarkin Kano Yace Yana Nan Tare Da Shugaba Buhari

Spread the love

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa biyayyarsa da hadin kansa ga shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari da kuma gwamnan Kano,Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba za su taba yin rawa ba.  Sarkin na Kano ya yi wannan bayani ne a ranar Talata data gabata a fadar gwamnatin Kano a dakin taro na Africa House a lokacin da shi da mukarrabansa suka kaiwa gwamna ziyara bisa al’ada.

Sarkin Kano yayi wadannan kalamai ne a Hawan Nasarawa, inda yace “Ina mai tabbatarwa da gwamnatin tarayya da gwamnatin Kano cewa, masarautar Kano za ta yi kokari wajen tabbatarda zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan Nijeriya. “Hadin kai shi ne ginshikin zaman lafiya daci gaban kowace al’umma. Ya zama wajibi mu kara kaimi wajen wayar da kawuna musamman na matasa ”

Sarki Sanusi ya yi kuma yi kira ga gwamnatin Kano data kai dauki ga manoman da suka gamu da ibtila’in kwari akan yabanyar gonakinsu tare kuma da yin kira ga musulmi da su ilmantu da darussan da ke cikin Ramadan sannan in sun ilmantu, su yi aiki da darussan da suka koya don kyautata rayuwarsu Sarki Sanusi ya kumayin kira da babbar murya kan batun fitar da tsare-tsare na wayar da kan matasa, inda ya ke cewa “Yana da matukar muhimmanci mu dauki gabarar wayar da kan matasanmu domin su fahimci muhimmancin zaman lafiya da hadin kai”

A nasa bangaren, gwamnan Kano,Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kira ya yi ga jama’ar Kano dasu zauna lafiya tsakaninsu da baki mazauna jihar, inda ya ke cewa“A Kano,baki mazauna jihar nan ‘yan uwan mune. A koda yaushe muna ganinsu a matsayin abokan cigaba.