Gwamnatin Najeriya Ta Fara Fitar Da Kayan Abinci Zuwa Turai

Spread the love

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce, daga yau Alhamis, za ta fara fitar da doyar da ake nomawa a kasar zuwa kasashen Turai a hukumance, in da ake matukar bukatar doyar. Ministan ayyukan noma na kasar Audu Ogbe ne, ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron Majalisar Ministocin kasar karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a birnin Abuja.

Mr. Ogbe ya ce, a tashin farko, za a fara fitar da tan 72 na doyra zuwa Birtaniya. Ministan ya ce, gabanin fara fitar da doyar a hukumance, Najeriya ta fitar da wani adadi na tan din doyar zuwa birnin New York na Amurka a ranar 16 ga wannan wata na Yuni. A cewar Minista Ogbe, kididdigar hukumar bunkasa aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta nuna cewa, Najeriya na samar da kashi 61 cikin 100 na doya a duk fadin duniya. Kasuwannin kasashen duniya na bukatar doyar da ake nomawa a Najeriya kamar yadda Ogbe ya bayyana,in da ya ce, abin kunya ne ga kasar ta gaza samar da doyar a kasuwannin. 

Gwamnatin Najeriya ta ce, akwai bukatar fitar da doyar saboda akasarin wadda ake nomawa na lalacewa ne saboda yalwarta a cikin gida Najeriya.