Amurka Ta fitar Da Sabbin Sharudda Akan Musulmi Masu Shiga Kasarta

Spread the love

Kamfanin dillancin Labaran Associated Press, yace ranar  Laraba ne  gwamnatin Donal Trump ta bada sanarwar kafa wannan sharadi ga kasashe Shidda da suka hada da Kasashen Iran, Libya, Somaliya, Sudan, Syria Da kasar Yemen. Sharadin Ya nuna cewa sai mutum yana da wani shakiki kamar yadda suka zayyana mai cikakken hankalai da zai tsaya masa kafin a amince masa shiga Amurka.

Sharuddan suna hada da cewa duk wani mai sha’awar Shiga Kasar sai ya kasance  yana da iyaye, ko Matarsa, Yaya, na miji ko mace wadanda suka kai shekarun sharia, suruki, surukuwa, da kuma wasu dangi na kusa.