Kwankwaso Ne Ya Dauki Nauyin Matasan Arewa Su Musgunawa Kabilar Igbo_ Inji Shugaban IPOB

Spread the love
 

Kungiyar ‘yan asalin  Biyafara wato IPOB, a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli suka mayar da martani kan wani zance da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso yayi, a kan ya kamata shugabannin kabilar Igbo su yi shika da masu fafutukar kafa Biyafara domin nuna gaskiya ga hadin kan kasa.

Sun bayyana cewa kalmomin tsohon gwamnan Kano da takun sa yana nuna goyon baya ne tallafawa ga shugabanin kungiyoyin matasan arewa da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku ficewa daga jihohin arewacin Najeriya.

Shafin Internet na Oaktv  ya rawaito cewa Wannan kalamin yafitone daga bakin sakataren harkokin watsa labarai ta kungiyar IPOB, Emma Powerful ya ce shugabannin kungiyar a duk duniya a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ba su tare da shugabannin kasar Igbo.

Sakataren ya ce: “Kwankwaso a yanzu haka ya bayyana mana manufarsa a cikin bayanin da yayi cewa yana daya daga cikin wasu dattawan arewa masu tallafawa matasan arewan don musguna wa ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a jihohin arewacin kasar.”