Ma’aikatan Haraji 300 Sun Ajiye Aiki A Kano

Spread the love

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa daruruwa Daga cikin ma’aikatan hukumar tara haraji da Gwamnatin jihar ta dauka aiki kwanakin baya sun ajiye aiki saboda karancin Albashi.
Kimanin watanni Uku kenan Gwamnatin Kano ta gudanar da taron yaye jami’ai 765 da ta dauka aiki a hukumar tara haraji ta jihar (KIRS) da nufin cimma kudurin hukumar na tara kudaden haraji akalla Naira Biliyan N10 duk karshen wata daga 2018.


Rahotanni sun tabbatar da cewa kawo yanzu kimanin mutum 300 daga cikinsu suka ajiye aikin sakamakon abinda suka kira rashin cika masu alkawurran da aka daukar masu ba a cikin yarjejeniyar aikin.
A wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano ana biyan jami’an albashin Naira 35 sabanin yadda sukayi tunani ganin cewa ance za’a rika biyansu albashi ninkin abunda suke karba a wuraren ayyukansu da suka baro.
Bayanai sun nuna galibin ma’aikatan sun kammala karatunsu na jami’a a yayin da wasunsu kuma ke matakin aiki (albashi) na 8, wasu kuma na 9 wasu kuma suna mataki na 10.
Duk yunkurin da majiyar tamu tayi don jin ta bakin shugaban hukumar tara kudaden haraji na jihar Kano, Sani Abubakar Dembo ya gagara kasancewar ance ya tafi Umara.