SARAKI YAYI NASARA AKAN GWAMNATIN TARAYYA

Spread the love

Kotun da’ar ma’aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Abubakar Bukola Saraki akan zargin boye gaskiyar kadarorin da ya mallaka, a shari’ar da aka kwashe lokaci mai tsawo ana tafkawa a kotu.

Alkalin kotun mai shari’a Danladi Umar ya bayyana cewa lauyoyin gwamnatin kasar nan da ke tuhumar wanda aka zarga a shari’ar, sun kasa gamsar da kotun cewa Sanata Saraki ya aikata laifin.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar hudu ga wannan watan ne dai shugaban majalisar dattawan kasar na ya shigar da bukatar cewa ba shi da laifin don haka kotu ta sallami karar tashi.