UWARGIDAN SHUGABA BUHARI BATA GA MIJINTA BA A LONDON

Spread the love

Wani rahoto da shafin jaridar Sahara Reporters ya fitar ya nuna cewa uwargidan shugaba Buhari, Hajia Aisha Buhari ba ta samu damar ganin maigidan na ta ba a ziyarar da ta kai masa birnin Landan inda ya ke jiyya. A cewar rahoton na Sahara Reporters, wata majiya ta bayyana cewa da yawa daga cikin ma’aikatan Shugaba Buhari basu san inda yakeba har da masu gadinsa.

Kamfanin jaridar ya kara da cewa shugaban kasa Buhari har ila yau bai yi magana da Farfesa Yemi Osinbajo a wayar tarho ba tun lokacin da ya fita daga kasar nan domin neman magani. Rahoton ya kara da cewa wasu makusanta Shugaba Muhammad Buhari su ke dakile ganin halin da Shugaban ke ciki, saboda gudun fitar wasu bayanai akan lafiyar shugaban, saboda ana zargin cewa shugaban kasa na fama da matsanancin ciwon daji.